English
A A A A A

Ayyukan Manzanni 7:44-60
44. “Kakanni-kakanninmu suna da Wuri mai tsarki na Shaida tare da su a hamada. An yi shi bisa ga yadda Allah ya umarci Musa, bisa ga zānen da ya gani.
45. Bayan sun gāji Wuri mai tsarkin nan, kakanninmu a ƙarƙashin jagorancin Yoshuwa suka kawo shi tare da su, lokacin da suka ƙwace ƙasar daga alʼumman da Allah ya kora a idanunsu. Wuri mai tsarki ɗin ya kasance a ƙasar har zamanin Dawuda,
46. wanda ya sami tagomashi daga Allah, ya kuma nemi yǎ yi wa Allah na Yaƙub wurin zama.
47. Amma Solomon ne ya gina masa gida.
48. “Duk da haka, Mafi Ɗaukaka ba ya zama a gidajen da mutane suka gina. Kamar yadda annabi ya faɗi cewa:
49. “ ‘Sama ne kursiyina, duniya kuma wurin ajiye tafin ƙafata. Wane irin gida za ka gina mini? Ko kuwa ina wurin hutuna zai kasance? In ji Ubangiji.
50. Ba hannuna ne ya yi dukan waɗannan abubuwa ba?’
51. “Ku mutane masu taurin kai, da zukata da kuma kunnuwa marasa kaciya! Kuna kama da kakanninku: Kullum kuna tsayayya da Ruhu Mai Tsarki!
52. An yi wani annabin da kakanninku ba su tsananta wa ba? Sun ma kashe waɗanda suka yi maganar zuwan Mai Adalcin nan. Yanzu kuwa kun bashe shi kuka kuma kashe shi— 
53. ku da kuka karɓi dokar da aka sa a aiki ta wurin malaʼiku amma ba ku yi biyayya da ita ba.”
54. Da suka ji haka, sai suka yi fushi suka ciji haƙoransu.
55. Amma Istifanus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dubi sama ya kuma ga ɗaukakar Allah, da Yesu kuma tsaye a hannun dama na Allah.
56. Ya ce, “Ga shi, na ga sama a buɗe da kuma Ɗan Mutum tsaye a hannun dama na Allah.”
57. Da jin haka sai suka tattoshe kunnuwansu, suka kuma yi ihu da ƙarfi sosai, suka aukar masa gaba ɗaya.
58. Suka ja shi zuwa bayan birnin suka kuma yi ta jifansa da duwatsu. Ana cikin haka, shaidun suka ajiye tufafinsu a wurin wani saurayi mai suna Shawulu.
59. Yayinda suke cikin jifansa, sai Istifanus ya yi adduʼa ya ce, “Ubangiji Yesu, ka karɓi ruhuna.”
60. Saʼan nan ya durƙusa ya ɗaga murya ya ce, “Ubangiji, kada ka riƙe wannan zunubi a kansu.” Da ya faɗi haka, sai ya yi barci.