A A A A A

Ayyukan Manzanni 7:22-43
22. Musa ya sami ilimi cikin dukan hikimar Masarawa ya kuma zama mai iko cikin magana da ayyuka.
23. “Da Musa ya cika shekara arbaʼin da haihuwa, sai ya yanke shawara yǎ ziyarci ʼyanʼuwansa Israʼilawa.
24. Ya ga ɗayansu yana shan wulaƙanci a hannun wani mutumin Masar, sai ya je ya kāre shi, ya rama masa ta wurin kashe mutumin Masar ɗin.
25. Musa ya yi tsammani mutanensa za su gane cewa, Allah yana amfani da shi don ya cece su, amma ba su gane ba.
26. Washegari, Musa ya sadu da Israʼilawa biyu suna faɗa. Ya yi ƙoƙari ya sasanta su, yana cewa, ‘Ku mutane, ku ʼyanʼuwa ne, don me kuke so ku cutar da juna?’
27. “Amma mutumin da yake wulaƙanta ɗayan, ya tura Musa a gefe ya ce, ‘Wa ya mai da kai mai mulki, da alƙali a kanmu?
28. Kana so ka kashe ni kamar yadda ka kashe mutumin Masar nan na jiya?’
29. Saʼad da Musa ya ji haka, sai ya gudu zuwa ƙasar Midiyan, inda ya yi baƙunci, ya kuma haifi ʼyaʼya biyu maza.
30. “Bayan shekaru arbaʼin suka wuce, sai malaʼika ya bayyana ga Musa cikin harshen wuta a ɗan itace a hamada kusa da Dutsen Sinai.
31. Saʼad da ya ga haka, ya yi mamakin abin da ya gani. Da ya yi kusa domin ya duba sosai, sai ya ji muryar Ubangiji ta ce:
32. ‘Ni ne Allahn kakanninka, Allah na Ibrahim, Ishaku, da kuma Yaƙub.’ Sai Musa ya yi rawan jiki don tsoro, bai kuwa yi karambanin dubawa ba.
33. “Saʼan nan Ubangiji ya ce masa, ‘Ka cire takalmanka; wurin da kake tsayen nan mai tsarki ne.
34. Hakika na ga wulaƙancin da ake yi wa mutanena a Masar. Na ji nishinsu na kuma sauka domin in ʼyantar da su. Yanzu ka zo, zan aike ka ka koma Masar.’
35. “Wannan Musa ɗin da suka ƙi suna cewa, ‘Wa ya mai da kai mai mulki da kuma alƙali?’ Allah da kansa ya aike shi, ta wurin malaʼikan da ya bayyana a gare shi a ɗan itace, yǎ zama mai mulkinsu, da kuma mai cetonsu.
36. Ya fitar da su daga Masar ya kuma yi ayyukan da abubuwan banmamaki a Masar, a Jan Teku, da kuma cikin hamada har shekara arbaʼin.
37. “Wannan Musa ne ya faɗa wa Israʼilawa cewa, ‘Allah zai aika muku wani annabi kamar ni daga cikin mutanenku.’
38. Ya kasance a cikin taron nan a hamada, tare da malaʼikan da ya yi magana da shi a Dutsen Sinai, da kuma tare da kakanninmu; ya kuma karɓi kalmomi masu rai don ya miƙa mana.
39. “Amma kakanninmu suka ƙi yin masa biyayya. A maimakon haka, sai suka ƙi shi a cikin zuciyarsu kuwa suka koma Masar.
40. Suka ce wa Haruna, ‘Ka yi mana allolin da za su yi mana jagora. Game da wannan Musa ɗin wanda ya fitar da mu daga Masar-ba mu san abin da ya faru da shi ba!’
41. A lokacin ne suka ƙera gunki mai siffar ɗan maraƙi. Suka kawo masa hadayu suka kuma yi bikin girmama abin da suka ƙera da hannuwansu.
42. Sai Amma Allah ya juya musu baya ya kuma ba da su ga bautar abubuwan da suke a sararin sama. Wannan ya yi daidai da abin da yake a rubuce a cikin littafin annabawa, cewa: “ ‘Kun kawo mini hadayu da sadakoki shekaru arbaʼin cikin, hamada, Ya gidan Israʼila?
43. Kun ɗaukaka gidan tsafin Molek, da tauraron allahnku Refan, gumakan da kuka ƙera don ku yi musu sujada. Saboda haka zan aike ku zuwa bauta’ gaba da Babilon.