A A A A A

Ayyukan Manzanni 7:1-21
1. Sai babban firist ya tambaye shi ya ce, “Waɗannan zargen gaskiya ne?”
2. Game da wannan ya amsa, ya ce: “ʼYanʼuwa da ubanni, ku saurare ni! Allah mai ɗaukaka ya bayyana ga kakanmu Ibrahim yayinda yake a ƙasar Mesofotamiya tukuna, kafin ya yi zama a Haran.
3. Allah ya ce, ‘Ka bar ƙasarka da kuma mutanenka, ka tafi ƙasar da zan nuna maka.’
4. “Saboda haka ya bar ƙasar Kaldiyawa ya kuma yi zama a Haran. Bayan mutuwar mahaifinsa, Allah ya aikar da shi wannan ƙasar da yanzu kuke zama.
5. Bai ba shi gādo a nan ba, ko taki ɗaya na ƙasa. Amma Allah ya yi masa alkawari cewa shi da zuriyarsa masu zuwa bayansa za su mallaki ƙasar, ko da yake a lokacin Ibrahim ba shi da yaro.
6. Allah ya yi magana da shi ta haka: ‘Zuriyarka za su yi baƙunci a wata ƙasar da ba tasu ba, za su yi bauta su kuma sha wulaƙanci har shekara ɗari huɗu.
7. Amma zan hore ƙasar da suka bauta wa.’ Allah ya ce, ‘kuma daga baya za su fita daga wannan ƙasa su kuma yi mini sujada a wannan wuri.’
8. Saʼan nan ya yi wa Ibrahim alkawari game da kaciya. Ibrahim kuwa ya zama mahaifin Ishaku ya kuma yi masa kaciya kwana takwas bayan haihuwarsa. Daga baya Ishaku ya zama mahaifin Yaƙub, Yaƙub kuma ya zama mahaifin kakanninmu sha biyun nan.
9. “Domin kakanninmu sun ji kishin Yusuf, sai suka sayar da shi bawa zuwa Masar. Amma Allah ya kasance tare da shi
10. ya kuma cece shi daga dukan wahalolinsa. Ya ba wa Yusuf hikima ya kuma sa ya sami farin jini a wurin Firʼauna, sarkin Masar; saboda haka ya mai da shi mai mulki a kan Masar da kuma dukan fadarsa.
11. “Sai yunwa ta auko wa dukan Masar da Kanʼana, ta kawo wahala mai tsanani, kakanninmu ba su iya samun abinci ba.
12. Saʼad da Yaƙub ya ji cewa akwai hatsi a Masar, sai ya aiki kakanninmu ziyararsu ta farko.
13. A ziyararsu ta biyu, Yusuf ya faɗa wa ʼyanʼuwansa wane ne shi, Firʼauna kuwa ya sami sani game da iyalin Yusuf.
14. Bayan wannan, Yusuf ya aika a zo da mahaifinsa Yaƙub da dukan iyalinsa, gaba ɗaya dai mutum sabaʼin da biyar ne.
15. Sai Yaƙub ya gangara zuwa Masar, inda shi da kuma kakanninmu suka mutu.
16. Aka dawo da gawawwakinsu Shekem aka binne su a kabarin da Ibrahim ya saya daga wurin ʼyaʼyan Hamor da waɗansu kuɗi a Shekem.
17. “Da lokaci ya yi kusa da Allah zai cika alkawarin da ya yi wa Ibrahim, sai yawan mutanenmu da suke a Masar ya ƙaru ƙwarai.
18. Saʼan nan wani sarki, wanda bai san kome game da Yusuf ba, ya zama mai mulkin Masar.
19. Ya kuwa wulaƙanta mutanenmu sosai, ya kuma gwada wa kakanni-kakanninmu azaba ta wurin tilasta su su zubar da sababbin jariransu, don su mutu.
20. “A lokacin nan aka haifi Musa, shi kuwa ba kamar sauran jarirai ba ne. Wata uku aka yi renonsa a gidan mahaifinsa.
21. Saʼad da aka ajiye shi a waje, diyar Firʼauna ta ɗauke shi ta kuma rene shi kamar ɗanta.