English
A A A A A

Ayyukan Manzanni 5:1-21
1. To wani mutum mai suna Ananiyas tare da matarsa Saffiratu, shi ma ya sayar da wata mallakarsa.
2. Da cikakken sanin matarsa ya ajiye sashi daga cikin kuɗin don kansa, ya kuma kawo sauran ya ajiye a sawun manzanni.
3. Sai Bitrus ya ce, “Ananiyas, ta yaya Shaiɗan ya cika zuciyarka haka da ka yi wa Ruhu Mai Tsarki ƙarya ka kuma ajiye wa kanka sauran kuɗin da ka karɓa na filin?
4. Ba naka ba ne kafin ka sayar da shi? Bayan da ka sayar da shi kuma, kuɗin ba naka ba ne? Me ya sa ka yi tunanin yin irin wannan abu? Ba mutum ne ka yi wa ƙarya ba, Allah ne ka yi masa.”
5. Da Ananiyas ya ji wannan, sai ya fāɗi ya mutu. Sai babbantsoro kuwa ya kama duk waɗanda suka ji abin da ya faru.
6. Sai samari suka zo gaba, suka naɗe gawarsa, suka fitar da shi suka je suka binne.
7. Bayan kusan awa uku, sai matarsa ta shigo, ba da sanin abin da ya faru ba.
8. Bitrus ya tambaye ta, ya ce, “Gaya mini, kuɗin da yake da Ananiyas kuka sayar da filin ke nan?” Ta ce, “I, haka ne muka sayar.”
9. Bitrus ya ce mata, “Ta yaya kuka yarda ku gwada Ruhun Ubangiji? Duba! Sawun mutanen da suka binne mijinki suna bakin ƙofa, za su kuwa ɗauke ki zuwa waje ke ma.”
10. Nan take ta fāɗi a ƙafafunsa ta mutu. Sai samarin suka shigo ciki, suka kuwa same ta matacciya, suka ɗauke ta suka kai ta waje suka binne ta kusa da mijinta.
11. Babbantsoro ya kama dukan ikkilisiya da kuma duk wanda ya ji game da abubuwan nan.
12. Manzannin suka yi ayyukan da alamu masu banmamaki masu yawa a cikin mutanen. Dukan masu bi kuwa sukan taru a Shirayin Solomon.
13. Ba wanda ya yi karambanin shiga cikinsu, duk da haka mutane suna girmama su ƙwarai.
14. Duk da haka, maza da matan da suke gaskata ga Ubangiji sai ƙaruwa suke, suka kuma ƙaru a yawa.
15. A sakamakon haka, mutane suka kawo marasa lafiya a tituna suka kwantar da su a kan gadaje da tabarmai domin aƙalla inuwar Bitrus za ta bi kan waɗansunsu yayinda yake wucewa.
16. Jamaʼa ma suka tattaru daga garuruwa kewaye da Urushalima suna kawo marasa lafiyarsu da kuma waɗanda mugayen ruhohi suke damun su, dukansu kuwa suka warke.
17. Sai babban firist da dukan abokan aikinsa, waɗanda suke na ƙungiyar Sadukiyawa suka cika da kishi.
18. Suka kama manzannin suka sa su a kurkukun da ake sa kowa da kowa.
19. Amma da dare wani malaʼikan Ubangiji ya buɗe ƙofofin kurkukun ya fitar da su.
20. Ya ce, “Ku je ku tsaya a filayen haikali ku sanar wa mutane cikakken saƙon wannan sabon rai.”
21. Da gari ya waye, sai suka shiga filayen haikali, yadda aka faɗa musu, suka kuwa fara koyar da mutane. Saʼad da babban firist da abokan aikinsa suka iso, sai suka kira Majalisa gaba ɗaya-dukan dattawan Israʼila-suka kuma aika kurkuku a zo da manzannin.