A A A A A

Ayyukan Manzanni 4:23-37
23. Da aka sake su, Bitrus da Yohanna suka koma wajen mutanensu suka ba da labarin duk abin da manyan firistoci da dattawa suka faɗa musu.
24. Saʼad da suka ji wannan, sai suka ɗaga muryoyinsu gaba ɗaya cikin adduʼa ga Allah, suka ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kai ka halicci sama da ƙasa da kuma teku, da kome da yake cikinsu.
25. Ka yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki ta bakin bawanka, kakanmu Dawuda cewa: “ ‘Don me ƙasashe suke fushi, mutane kuma suke ƙulla shawara a banza?
26. Sarakunan duniya sun ja dāgā, masu mulki kuma sun taru gaba ɗaya, suna gāba da Ubangiji da kuma Shafaffensa.’
27. Hakika Hiridus da Buntus Bilatus suka haɗu tare da Alʼummai da kuma mutanen Israʼila a wannan birni ne don su ƙulla gāba da bawanka mai tsarki Yesu, wanda ka shafe.
28. Sun aikata abin da ikonka da kuma nufinka ya riga ya shirya tuntuni zai faru.
29. Yanzu, Ubangiji, ka dubi barazanansu ka kuma sa bayinka su furta maganarka da iyakar ƙarfin hali.
30. Ka miƙa hannunka don ka warkar ka kuma yi ayyukan banmamaki da alamu masu banmamaki ta wurin sunan bawanka mai tsarki Yesu.”
31. Bayan suka yi adduʼa, sai inda suka taru ya jijjigu. Dukansu kuwa suka ciku da Ruhu Mai Tsarki, suka yi ta shaidar maganar Allah babu tsoro.
32. Dukan masu bi kuwa zuciyarsu ɗaya ne, nufinsu kuwa ɗaya. Babu wani da ya ce abin da ya mallaka nasa ne, amma sun raba kome da suke da shi.
33. Da iko mai ƙarfi manzanni suka ci gaba da shaidar tashin matattu na Ubangiji Yesu, alheri mai yawa kuwa yana bisansu duka.
34. Babu mabukata a cikinsu. Lokaci lokaci waɗanda suke da gonaki ko gidaje sukan sayar da su, su kawo kuɗi daga abin da suka sayar,
35. su ajiye a sawun manzannin, a kuma raba wa kowa gwargwadon bukatarsa.
36. Yusuf, wani Balawe daga Saifurus, wanda manzanni suke kira Barnabas (wanda yake nufin Ɗan Ƙarfafawa)
37. ya sayar da wata gonar da ya mallaki ya kuma kawo kuɗin ya ajiye a sawun manzanni.