A A A A A

Yohanna 12:27-50
27. “Yanzu kuwa na damu, amma me zan ce? ‘Uba, ka cece ni daga wannan saʼa’? Aʼa, ai, saboda wannan dalili ne na kai wannan saʼa.
28. Uba, ka ɗaukaka sunanka!” Sai wata murya ta fito daga sama ta ce, “Na riga na ɗaukaka shi, zan kuma ƙara ɗaukaka shi.”
29. Taron da suke a wurin suka ji, suka ce an yi tsawa; waɗansu kuwa suka ce malaʼika ne ya yi masa magana.
30. Yesu ya ce, “An yi wannan muryar saboda amfaninku ne, ba don nawa ba.
31. Yanzu ne za a yi wa duniyan nan shariʼa, yanzu ne za a tumɓuke mai mulkin duniyan nan.
32. Amma ni, saʼad da an ɗaga ni daga ƙasa, zan ja dukan mutane gare ni.”
33. Ya faɗa haka ne don yǎ nuna irin mutuwar da zai yi.
34. Sai taron suka ce, “Ahab, Dokarmu ta ce, Kiristi zai kasance har abada, to, yaya za ka ce, ‘Dole ne a ɗaga Ɗan Mutum?’ Wane ne wannan ‘Ɗan Mutum’?”
35. Sai Yesu ya faɗa musu, “Haske zai kasance da ku na ɗan lokaci. Ku yi tafiya yayinda hasken yana nan tare da ku, kada duhu yǎ cim muku. Mai tafiya a cikin duhu bai san inda za shi ba.
36. Ku dogara ga hasken yayinda kuke da shi, don ku zama ʼyaʼyan haske.” Da Yesu ya gama magana, sai ya tafi ya ɓuya daga gare su.
37. Ko bayan Yesu ya yi dukan waɗannan abubuwan banmamaki a gabansu, duk da haka ba su gaskata da shi ba.
38. Wannan ya faru ne, don a cika maganar annabi Ishaya cewa: “Ubangiji, wa ya gaskata saƙonmu, ga wa kuma aka bayyana hannun ikon Ubangiji?”
39. Saboda haka ba su iya gaskatawa ba, domin, kamar yadda Ishaya ya faɗa a wani wuri cewa:
40. “Ya makantar da idanunsu ya kuma taurare zukatansu, don kada su gani da idanunsu, ko su fahimta a zukatansu, ko kuwa su juyo-har in warkar da su.”
41. Ishaya ya faɗi haka ne, saboda ya hangi ɗaukakar Yesu, ya kuwa yi magana a kansa.
42. Duk da haka, da yawa har daga cikin shugabanni ma suka gaskata da shi. Amma saboda Farisiyawa ba su furta bangaskiyarsu ba, don tsoron kada a kore su daga majamiʼa;
43. gama sun fi son yabon mutane, fiye da yabon Allah.
44. Saʼan nan Yesu ya ɗaga murya ya ce, “Duk wanda ya gaskata da ni, ba ni yake gaskatawa ba, amma ga wanda ya aiko ni ne.
45. Duk mai dubana, yana duban wanda ya aiko ni ne.
46. Na zo cikin duniya a kan ni haske ne, don duk wanda ya gaskata da ni, kada yǎ zauna a cikin duhu.
47. “Duk mai jin kalmomina bai kuwa kiyaye su ba, ba ni ba ne nake shariʼanta shi. Gama ban zo domin in yi wa duniya shariʼa ba, sai dai domin in cece ta.
48. Akwai mai hukunci saboda wanda ya ƙi ni, bai kuma karɓi kalmomina ba; wannan maganar da na faɗa ita ce za ta hukunta shi a rana ta ƙarshe.
49. Gama ba don kaina na yi magana ba, Uban da ya aiko ni shi kansa ne ya ba ni umarni a kan abin da zan faɗa da kuma yadda zan faɗe shi.
50. Na san cewa umarninsa yana kai ga rai madawwami. Saboda haka duk abin da na faɗa na faɗe shi ne kamar dai yadda Uba ya ce in faɗa.”