English
A A A A A

Ayyukan Manzanni 4:1-22
1. Sai firistoci da shugaban masu gadin haikalin da kuma Sadukiyawa suka hauro wurin Bitrus da Yohanna yayinda suke cikin magana da mutane.
2. Sun damu ƙwarai da gaske domin manzannin suna koya wa mutane suna kuma shela a cikin Yesu cewa akwai tashin matattu.
3. Sai suka kama Bitrus da Yohanna, amma da yake yamma ta riga ta yi sai suka sa su cikin kurkuku sai washegari.
4. Amma da yawa da suka ji saƙon suka gaskata, yawan mutanen kuwa ya ƙaru ya kai wajen dubu biyar.
5. Washegari, sai masu mulki, dattawa da kuma malaman dokoki suka taru a Urushalima.
6. Annas babban firist yana nan, haka ma Kayifas Yohanna, Alekzanda da kuma sauran mutanen da suke iyalin babban firist.
7. Suka sa aka kawo Bitrus da Yohanna a gabansu suka kuma fara yin musu tambayoyi cewa: “Da wane iko ko da wane suna kuka yi wannan?”
8. Sai Bitrus, cike da Ruhu Mai Tsarki ya ce musu: “Masu mulki da dattawan mutane!
9. In ana tuhumarmu ne yau saboda alherin da aka yi wa gurgun nan da kuma yadda aka warkar da shi,
10. to, sai ku san wannan, ku da dukan mutanen Israʼila cewa: Da sunan Yesu Kiristi Banazare, wanda kuka gicciye amma wanda Allah ya tasar daga matattu ne, wannan mutum yake tsaye a gabanku lafiyayye.
11. Shi ne, “ ‘dutsen da ku magina kuka ƙi, wanda kuwa ya zama dutsen kusurwar gini.’
12. Ba a samun ceto ta wurin wani dabam, gama babu wani suna a ƙarƙashin sama da aka ba wa mutane wanda ta wurinsa dole mu sami ceto.”
13. Da suka ga ƙarfin halin Bitrus da Yohanna suka kuma gane cewa su marasa ilimi ne, talakawa kuma, sai suka yi mamaki suka kuma lura cewa waɗannan mutane sun kasance tare da Yesu.
14. Amma da yake sun ga mutumin da aka warkar yana tsaye a wurin tare da su, sai suka rasa abin faɗi.
15. Saboda haka suka umarta a fitar da su daga Majalisar, saʼan nan suka yi shawara da juna.
16. Suka ce, “Me za mu yi da waɗannan mutane? Kowa da yake zama a Urushalima ya san sun yi abin banmamaki, kuma ba za mu iya yin mūsu wannan ba.
17. Amma don a hana wannan abu daga ƙara bazuwa cikin mutane, dole mu kwaɓe mutanen nan kada su ƙara yi wa kowa magana cikin wannan suna.”
18. Sai suka sāke kiransu ciki suka kuma umarce su kada su kuskura su yi magana ko su ƙara koyarwa a cikin sunan Yesu.
19. Amma Bitrus da Yohanna suka amsa, “Ku shariʼanta da kanku ko daidai ne a gaban Allah mu yi muku biyayya maimakon Allah.
20. Gama ba za mu iya daina yin magana game da abin da muka gani muka kuma ji ba.”
21. Bayan ƙarin barazana sai suka bar su su tafi. Ba su iya yanke shawara yadda za a hore su ba, domin dukan mutane suna yabon Allah saboda abin da ya faru.
22. Gama mutumin da ya sami warkarwar banmamaki, shekarunsa sun fi arbaʼin.