A A A A A

Ayyukan Manzanni 2:22-47
22. “Mutanen Israʼila, ku saurari wannan: Yesu Banazare shi ne mutumin da Allah ya tabbatar muku ta wurin muʼujizai, ayyukan banmamaki, da kuma alamu, waɗanda Allah ya yi a cikinku ta wurinsa, kamar yadda ku kanku kuka sani.
23. An ba da wannan mutum gare ku bisa ga nufin Allah da kuma rigyasaninsa, ku kuma tare da taimakon mugayen mutane, kuka kashe shi ta wurin kafa shi a kan gicciye.
24. Amma Allah ya tashe shi daga matattu, ya ʼyantar da shi daga azabar mutuwa, don ba ya yiwuwa mutuwa ta riƙe shi.
25. Dawuda ya yi faɗi game da shi, cewa: “ ‘Kullum ina ganin Ubangiji a gabana. Domin yana a hannuna na dama, ba zan jijjigu ba.
26. Saboda haka, zuciyata na farin ciki, harshena kuma na murna, jikina kuma zai kasance da bege,
27. gama ba za ka bar ni cikin kabari ba, ba kuwa za ka yarda Mai Tsarkinka yǎ ruɓa ba.
28. Ka sanar da ni hanyoyin rai, za ka cika ni da farin ciki a gabanka.’
29. “ʼYanʼuwa, zan iya tabbatar muku gabagaɗi cewa kakanmu Dawuda ya mutu aka kuma binne shi, kabarinsa kuwa yana a nan har yǎ zuwa yau.
30. Amma shi annabi ne ya kuma san abin da Allah ya yi masa alkawari da rantsuwa cewa zai ɗora ɗaya daga cikin zuriyarsa a kan gadon sarautarsa.
31. Ganin abin da yake gaba, ya yi magana a kan tashin Kiristi daga matattu cewa, ba a bar shi a kabari ba, jikinsa kuma bai ruɓa ba.
32. Allah ya tashe wannan Yesu zuwa rai, mu kuwa duk shaidu ne ga wannan.
33. An ɗaukaka shi zuwa ga hannun dama na Allah, ya karɓi alkawarin Ruhu Mai Tsarki daga Uba, ya kuma zubo abin da yanzu kuke gani kuke kuma ji.
34. Gama Dawuda bai hau zuwa sama ba, duk da haka ya ce, “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina: “Zauna a hannun damana,
35. sai na mai da abokan gābanka matashin sawunka.” ’
36. “Saboda haka bari dukan Israʼila su tabbatar da wannan: Allah ya mai da wannan Yesu, da kuka gicciye, Ubangiji da kuma Kiristi.”
37. Saʼad da mutane suka ji wannan, sai suka soku a zuci sai suka ce wa Bitrus da sauran manzanni, “Yanʼuwa, me za mu yi?”
38. Bitrus ya amsa, “Ku tuba a kuma yi muku baftisma, kowannenku a cikin sunan Yesu Kiristi domin gafarar zunubanku. Za ku kuwa karɓi kyautar Ruhu Mai Tsarki.
39. Alkawarin dominku ne da ʼyaʼyanku da kuma dukan waɗanda suke da nesa-domin dukan waɗanda Ubangiji Allahnmu zai kira.”
40. Da waɗansu kalmomi masu yawa ya gargaɗe su; ya kuma roƙe su cewa, “Ku ceci kanku daga wannan lalataccen zamani.”
41. Waɗanda suka yarda da saƙonsa kuwa aka yi musu baftisma, a ranar kuwa yawansu ya ƙaru da mutum kusan dubu uku.
42. Suka ba da kansu ga koyarwar manzanni da kuma ga zumunci, ga gutsuttsura burodin da kuma ga adduʼa.
43. Kowa ya cika da tsoro, manzannin kuwa suka aikata abubuwan banmamaki da alamu masu yawa.
44. Dukan masu bi suna tare, suna kuma mallakar kome tare.
45. Suka dinga sayar da ƙaddarorinsu da kayayyakinsu, suka ba wa kowa gwargwadon bukatarsa.
46. Kowace rana suka ci gaba da taruwa a filin haikali. Suka gutsuttsura burodi a gidajensu suna cin abinci tare da farin ciki da zuciya ɗaya,
47. suna yabon Allah suna kuma samun tagomashin dukan mutane. Ubangiji kuwa ya ƙara yawansu kowace rana na waɗanda suke samun ceto.