A A A A A

Ayyukan Manzanni 2:1-21
1. Da ranar Fentikos ta yi, dukansu suna tare wuri ɗaya.
2. Ba zato ba tsammani sai aka ji motsi kamar ta babbar iska tana hurowa daga sama ta kuma cika dukan gidan da suke zaune.
3. Suka ga wani abin da ya yi kama da harsunan wuta, suka rarrabu suna kuma sassauka a kan kowannensu.
4. Dukansu kuwa suka cika da Ruhu Mai Tsarki suka kuma fara magana da waɗansu harsuna yadda Ruhu ya sa suka iya.
5. To, a Urushalima akwai Yahudawa masu tsoron Allah, daga kowace ƙasa a duniya.
6. Da suka ji wannan motsi, taro ya haɗu wuri ɗaya a ruɗe, domin kowannensu ya ji suna magana da yarensa.
7. Cike da mamaki, suka yi tambaya suna cewa: “Ashe, duk waɗannan mutane masu magana ba Galiliyawa ba ne?
8. To, yaya kowannenmu yana ji suna yarensa?
9. Fartiyawa, Medes da Elamawa; mazaunan Mesofotamiya, Yahudiya da Kaffadokiya, Fontus da Asiya,
10. Firjiya da Famfiliya, Masar da sassa Libiya kusa da Sairin; baƙi daga Roma
11. (Yahudawa da kuma waɗanda suka tuba suka shiga Yahudanci); Kiretawa da Larabawa-mun ji su suna shelar abubuwan banmamaki na Allah da yarenmu!”
12. A ruɗe kuma cike da mamaki, suka tambayi junansu cewa, “Mene ne wannan yake nufi?”
13. Duk da haka waɗansu suka yi musu baʼa suka ce, “Sun yi tatil da ruwan inabi ne.”
14. Sai Bitrus ya miƙe tsaye tare da Sha Ɗayan nan, ya ɗaga muryarsa ya yi wa taron jawabi ya ce: “ʼYanʼuwana Yahudawa da dukanku da kuke zama cikin Urushalima, bari in bayyana muku wannan: ku saurara da kyau ga abin da zan faɗa.
15. Waɗannan mutane ba su bugu ba, kamar yadda kuka ɗauka. Yanzu ƙarfe tara na safe ne kawai!
16. Aʼa, ai, abin da aka yi magana ta bakin annabi Yowel ke nan cewa:
17. “Allah ya ce, ‘A kwanakin ƙarshe, zan zubo Ruhuna bisa dukan mutane. ʼYaʼyanku maza da mata za su yi annabci, samarinku za su ga wahayoyi, dattawanku kuma za su yi mafarkai.
18. Kai, har ma a kan bayina, maza da mata, zan zubo Ruhuna a waɗancan kwanaki, za su kuwa yi annabci.
19. Zan nuna abubuwan banmamaki a sararin sama da alamu a nan ƙasa, jini da wuta da kuma hauhawan hayaƙi.
20. Za a mai da rana duhu, wata kuma ya zama jini, kafin zuwa rana mai girma da kuma ta ɗaukaka ta Ubangiji.
21. Kuma duk wanda ya kira bisa sunan Ubangiji zai sami ceto.’