A A A A A

Yohanna 19:1-22
1. Saʼan nan Bilatus ya tafi da Yesu ya kuma sa aka yi masa bulala.
2. Sai sojojin suka tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa a kā, suka kuma yafa masa wata riga mai launin shunayya.
3. Suka yi ta zuwa wurinsa suna cewa, “Ranka yǎ daɗe, sarkin Yahudawa!” Suna ta marinsa a fuska.
4. Bilatus kuwa ya sāke fitowa ya ce wa Yahudawa, “Ga shi, zan fito muku da shi don ku san cewa ban same shi da wani abin zargi ba.”
5. Saʼad da Yesu ya fito sanye da rawanin ƙayar da kuma riga mai launin shunayya, sai Bilatus ya ce musu, “Ga mutumin!”
6. Nan da nan da manyan firistoci da maʼaikatansu suka gan shi, sai suka yi ihu suka ce, “A gicciye! A gicciye!” Amma Bilatu ya amsa, ya ce, “Ku, ku ɗauke shi ku gicciye. Ni dai ban same shi da wani abin zargi ba.”
7. Yahudawa dai suka nace suna cewa, “Mu fa muna da doka, kuma bisa ga dokar dole yǎ mutu domin ya mai da kansa Ɗan Allah.”
8. Da Bilatus ya ji haka, sai tsoro ya ƙara kama shi,
9. sai ya sāke koma cikin fada. Ya tambayi Yesu, “Daga ina ka fito?” Amma Yesu bai amsa masa ba.
10. Bilatus ya ce, “Ba za ka yi mini magana ba? Ba ka san cewa ina da ikon sakinka, ko gicciye ka ba?”
11. Yesu ya amsa, ya ce, “Ba ka da wani iko a kaina, in ba a ba ka daga sama ba. Saboda haka wanda ya bashe ni gare ka, ya fi na zunubi.”
12. Daga nan fa, Bilatus ya yi nemi yǎ saki Yesu, sai dai Yahudawa suka yi ta ihu suna cewa, “In ka saki wannan mutum, kai ba abokin Kaisar ba ne. Duk wanda ya ɗauka kansa a matsayin sarki, ai, yana gāba da Kaisar ne.”
13. Da Bilatus ya ji haka, sai ya fito da Yesu, ya kuma zauna a kujerar shariʼar da ake ce da shi Daɓen Dutse (wanda a harshen Aramayik ana ce da shi Gabbata).
14. Ranar Shirye-shiryen Makon Bikin Ƙetarewa ce kuwa, wajen saʼa ta shida. Sai Bilatus ya ce wa Yahudawa, “Ga sarkinku.”
15. Amma suka yi ihu suka ce, “A yi da shi! A yi da shi! A gicciye shi!” Bilatus ya ce, “A! In gicciye sarkinku?” Sai manyan firistoci suka amsa suka ce, “Mu dai, ba mu da wani sarki sai Kaisar.”
16. A ƙarshe Bilatus ya ba da shi gare su a gicciye shi. Saboda haka sojoji suka tafi da Yesu.
17. Ɗauke da gicciyensa, ya kuwa fita zuwa wurin Ƙoƙon Kai, (wanda a harshen Aramaya ana ce da shi Golgota.)
18. Nan suka gicciye shi tare da waɗansu mutum biyu-ɗaya a kowane gefe da Yesu a tsakiya.
19. Bilatus ya sa aka rubuta wata sanarwa aka kafa a kan gicciyen. Abin da aka rubuta kuwa shi ne: “YESU BANAZARE, SARKIN YAHUDAWA.”
20. Yahudawa da yawa suka karanta wannan sanarwa, gama inda aka gicciye Yesu yana kusa da birni. An kuwa rubuta sanarwar da Aramayanci, Romanci da kuma Helenanci.
21. Sai manyan firistocin Yahudawa suka ce, “Aʼa! Kada ka rubuta, ‘Sarkin Yahudawa,’ ka dai rubuta, wannan mutum ya ce shi sarkin Yahudawa ne.”
22. Bilatus ya amsa, ya ce, “Abin da na rubuta, na rubuta.”