A A A A A

Yohanna 18:19-40
19. Ana cikin haka, sai babban firist ya tuhumi Yesu game da almajiransa da kuma koyarwarsa.
20. Yesu ya amsa, ya ce, “Ai, na yi wa duniya magana a fili. Na kuma sha yin koyarwa a majamiʼu ko kuma a haikali inda Yahudawa duka sukan taru. Ban taɓa faɗin kome a ɓoye ba.
21. Don me kake tuhumata? Ka tambayi waɗanda suka ji ni. Ba shakka, sun san abin da na faɗa.”
22. Da Yesu ya faɗa haka, sai ɗaya daga cikin maʼaikatan da yake tsaye kusa ya mare shi a fuska ya ce, “Haka za ka amsa wa babban firist?”
23. Yesu ya amsa, ya ce, “In na faɗi abin da ba daidai ba, ka nuna abin da ba daidai ba. Amma in gaskiya na faɗa, don me ka mare ni?”
24. Sai Annas ya aika da shi, a ɗaure, wurin Kayifas babban firist.
25. Da Siman Bitrus yana nan tsaye yana jin ɗumin wuta, sai aka tambaye shi, “Kai, kai ma ba ɗaya daga cikin almajiransa ba ne?” Sai ya yi mūsu, yana cewa, “Sam, ba na ciki.”
26. Sai wani daga cikin bayin babban firist dangin wanda Bitrus ya sare wa kunne, ya tambaya shi ya ce, “Kana tsammani ban gan ka tare da shi a gonar zaitun ba?”
27. Bitrus ya sāke yin mūsu, nan take kuwa zakara ya yi cara.
28. Saʼan nan Yahudawa suka fitar da Yesu daga wurin Kayifas zuwa fadar gwamnar Roma. A yanzu dai, safiya ta yi, don gudu kada su ƙazantar da kansu Yahudawa ba su shiga cikin fadar ba; sun so su iya ci Bikin Ƙetarewa.
29. Saboda haka Bilatus ya fito wajensu ya ce, “Wace ƙara kuke kawowa game da mutumin nan?”
30. Suka amsa suka ce, “Da a ce shi ba mai laifi ba ne, ai, da ba mu bashe shi gare ka ba.”
31. Bilatus ya ce, “Ku tafi da shi da kanku mana, ku hukunta shi bisa ga dokarku.” Sai Yahudawa suka ƙi suka ce, “Ba mu da ikon yanke wa wani hukuncin kisa.”
32. Wannan kuwa ya faru ne don a cika kalmomin da Yesu ya yi da suka nuna irin mutuwar da zai yi.
33. Sai Bilatus ya koma cikin fada, ya kira Yesu ya tambaye shi, “Shin, kai ne sarkin Yahudawa?”
34. Yesu ya yi tambaya, ya ce, “Wannan raʼayin kanka ne, ko waɗansu ne suka yi maka magana game da ni?”
35. Bilatus ya amsa, ya ce, “Ni Bayahude ne? Ai, mutanenka ne da kuma manyan firistoci suka bashe ka gare ni. Me ka yi?”
36. Yesu ya ce, “Mulkina ba na duniyan nan ba ne. Da na duniyan nan ne da bayina sun yi yaƙi su hana Yahudawa kama ni. Amma fa mulkina daga wani waje ne.”
37. Sai Bilatus ya ce, “To, wato, kai sarki ne!” Yesu ya amsa, ya ce, “Haka yake, ni sarki ne yadda ka faɗa. Tabbatacce, saboda wannan dalili ne aka haife ni, kuma don wannan ne na zo duniya, domin in shaidi gaskiya. Duk wanda yake gefen gaskiya yakan saurare ni.”
38. Bilatus ya tambaye shi ya ce, “Mece ce gaskiya?” Da ya faɗi haka, sai ya sāke fitowa wurin Yahudawa ya ce, “Ni fa ban sami wani abin zargi game da shi ba.
39. Amma fa kuna da wata alʼada in lokacin Bikin Ƙetarewa ya yi, nakan sakar muku da ɗan kurkuku ɗaya. To, kuna so in sakar muku ‘sarkin Yahudawa’?”
40. Sai suka ɗau kururuwa suna cewa, “Kai, ba shi ba! A ba mu Barabbas!” To, Barabbas ɗin nan yana da hannu dumu-dumu a wani tawaye.