A A A A A

Yohanna 12:1-26
1. Kwana shida kafin Bikin Ƙetarewa, sai Yesu ya iso Betani, inda Lazarus yake, wanda Yesu ya ta da daga matattu.
2. A nan aka shirya abincin yamma don girmama Yesu. Marta ta ce yi hidima, Lazarus kuma yana ɗaya cikin waɗanda suke ci tare shi.
3. Sai Maryamu ta ɗauki wajen awo guda na nardi tsantsa, turare mai tsada; ta zuba a ƙafafun Yesu ta kuma goge ƙafafunsa da gashinta. Gidan duk ya cika da ƙanshin turaren.
4. Amma ɗaya daga cikin almajiransa, Yahuda Iskariyot, wanda daga baya zai bashe shi, bai amince ba, ya ce,
5. “Don me ba a sayar da turaren nan aka kuma ba da kuɗin ga matalauta ba? Ai, kuɗin ya kai albashin shekara guda.”
6. Ya yi wannan magana ba don ya kula da matalauta ba ne, sai dai don shi ɓarawo ne. Da yake shi ne mai ajiya jakar kuɗin, yakan taimaki kansa da abin da aka sa a ciki.
7. Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta, an nufa ta ajiye wannan turaren don ranar janaʼizata.
8. Kullum za ku kasance da matalauta, amma ba kullum za ku kasance tare da ni ba.”
9. Ana cikin haka sai babban taron Yahudawa suka sami labari Yesu yana can suka kuwa zo, ba kawai don shi ba amma don su kuma ga Lazarus, wanda ya ta da daga matattu.
10. Saboda haka manyan firistoci suka ƙulla su kashe Lazarus shi ma,
11. gama dalilinsa Yahudawa da yawa suna komawa ga Yesu suna kuma ba da gaskiya gare shi.
12. Washegari babban taron da suka zo Bikin suka sami labari cewa Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima.
13. Sai suka ɗaɗɗauko rassan dabino suka fiffita taryensa, suna ɗaga murya suna cewa, “Hosanna!” “Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!” “Mai albarka ne Sarkin Israʼila!”
14. Yesu ya sami ɗan jaki, ya hau, kamar yadda yake a rubuce cewa,
15. “Kada ki ji tsoro, Ya Diyar Sihiyona; duba, ga sarkinki yana zuwa, zaune a kan aholaki jaki.”
16. Da fari almajiransa ba su gane dukan wannan ba. Sai bayan da aka ɗaukaka Yesu, saʼan nan suka gane cewa an rubuta waɗannan abubuwa game da shi ne, har ma suka yi masa waɗannan abubuwa.
17. Taron da suke tare da shi a saʼad da ya kira Lazarus daga kabari ya kuma ta da shi daga matattu suka yi ta baza labarin.
18. Mutane da yawa kuwa suka fita taryensa, saboda sun ji labarin abin banmamakin da ya yi.
19. Saboda haka Farisiyawa suka ce wa juna, “Duba, wannan ba ya kai mu koʼina. Ga shi, duk duniya tana binsa!”
20. To, akwai waɗansu Helenawa a cikin waɗanda suka haura don su yi sujada a Bikin.
21. Suka zo wurin Filibus, wanda yake daga Betsaida ta Galili, da roƙo. Suka ce, “Ranka yǎ daɗe, muna so mu ga Yesu.”
22. Sai Filibus ya je ya gaya wa Andarawus, Andarawus da kuma Filibus suka gaya wa Yesu.
23. Yesu ya amsa, ya ce, “Lokaci ya yi da za a ɗaukaka Ɗan Mutum.
24. Gaskiya nake gaya muku, sai ƙwayar alkama ta fāɗi ƙasa ta mutu, in ba haka ba za ta kasance ƙwaya ɗaya tak. Amma in ta mutu, za ta ba da ʼyaʼya da yawa.
25. Duk mai ƙaunar ransa, zai rasa shi, duk mai ƙin ransa a wannan duniya, zai kiyaye shi har yǎ zuwa rai madawwami.
26. Duk wanda zai bauta mini dole yǎ bi ni, inda kuma nake, a can bawana zai kasance. Ubana zai girmama wanda yake bauta mini.