English
A A A A A

Luka 24:36-53
36. Suna cikin wannan zance, sai ga Yesu da kansa tsaye a tsakiyarsu. Sai ya ce musu, “Salama a gare ku!”
37. Suka firgita, suka tsorota, suna tsammani fatalwa ce suka gani.
38. Sai ya ce musu, “Don me kuke damuwa, kuma kuna shakka a zuciyarku?
39. Ku duba hannuwana da ƙafafuna. Ai, ni ne da kaina! Ku taɓa ni ku ji, ai, fatalwa ba ta da nama da ƙashi, yadda kuke gani nake da su.”
40. Da ya faɗi haka, sai ya nuna musu hannuwansa da ƙafafunsa.
41. Kuma har yanzu, suna cikin rashin gaskatawa, saboda murna da mamaki, sai ya tambaye su, “Ko kuna da abinci a nan?”
42. Suka ba shi ɗan gasashen kifi.
43. Ya karɓa ya ci a gabansu.
44. Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da na gaya muku tun ina tare da ku, cewa, dole a cika kome da aka rubuta game da ni, a cikin Dokar Musa, da Annabawa, da kuma Zabura.”
45. Sai ya wayar da tunaninsu don su fahimci Nassi.
46. Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da aka rubuta, cewa: Dole ne Kiristi ya sha wahala, a rana ta uku kuma ya tashi daga matattu.
47. Kuma a cikin sunansa za a yi waʼazin tuba da gafarar zunubai, ga dukan ƙassashe. Za a kuwa fara daga Urushalima.
48. Ku ne shaidu na waɗannan abubuwa.
49. Zan aika muku da abin da Ubana ya yi alkawari. Amma ku dakata a birnin tukuna, sai an rufe ku da iko daga sama.”
50. Bayan ya kai su waje kusa da Betani, sai ya ɗaga hannuwansa ya sa musu albarka.
51. Yana cikin sa musu albarka, sai ya rabu da su. Aka ɗauke shi zuwa cikin sama.
52. Sai suka yi masa sujada, suka koma Urushalima cike da murna sosai.
53. Sai suka ci gaba da zama a cikin haikalin, suna yabon Allah.