English
A A A A A

Luka 24:1-35
1. Da sassafe a ranar farko ta mako, matan suka je kabarin, da kayan ƙanshin da suka shirya.
2. Suka iske an riga an gungurar da dutsen daga bakin kabarin.
3. Amma da suka shiga ciki, ba su iske jikin Ubangiji Yesu ba.
4. Yayinda suna cikin tunani a kan wannan, nan take, ga waɗansu mutum biyu tsaye kusa da su, sanye da kaya masu ƙyalli, kamar walƙiya.
5. A cikin tsoro, matan suka fāɗi da fuskokinsu a ƙasa, amma mutanen suka ce musu, “Me ya sa kuke neman mai rai a cikin matattu?
6. Ba ya nan, ya tashi! Ku tuna yadda ya gaya muku tun yana tare da ku a Galili, cewa,
7. ‘Dole ne a ba da Ɗan Mutum ga hannun mutane masu zunubi, a kuma gicciye shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.’ ”
8. Sai suka tuna da maganarsa.
9. Da suka dawo daga kabarin, sai suka faɗa wa Sha Ɗayan nan da sauransu, dukan waɗannan abubuwa.
10. Matan da suka gaya wa manzannin waɗannan abubuwa su ne, Maryamu Magdalin, da Yowanna, da Maryamu uwar Yaƙub, da waɗansu da suke tare da su.
11. Amma ba su gaskata matan ba, domin sun ɗauki kalmominsu wani zancen banza ne.
12. Duk da haka, Bitrus ya tashi a guje zuwa kabarin. Da ya sunkuya, sai ya ga ƙyallayen lilin kaɗai a kwance. Sai ya koma yana tunani a ransa, a kan abin da ya faru.
13. A wannan rana kuma, biyu daga cikinsu suna tafiya zuwa wani ƙauye, da ake kira Emmawus, da suke kusan mil bakwai daga Urushalima.
14. Suna magana da juna a kan dukan abubuwan da suka faru.
15. Da suna magana, kuma suna tattauna waɗannan abubuwa da junansu, sai Yesu da kansa ya zo yana tafiya tare da su.
16. Amma ba a ba su ikon gane shi ba.
17. Sai ya tambaye, su ya ce, “Mene ne ku tattaunawa da juna a cikin tafiyarku?” Suka tsaya shiru, da damuwa a fuskarsu.
18. Ɗaya daga cikinsu, mai suna Kiliyobas, ya tambaye shi, ya ce, “Ashe, kai baƙo ne a Urushalima, da ba ka san abubuwan da suka faru a can, a cikin kwanakin nan ba?”
19. Sai ya yi tambaya, “Waɗanne abubuwa?” Suka amsa suka ce, “Game da Yesu Banazare. Shi annabi ne, mai iko ne kuma cikin ayyukansa da maganarsa, a gaban Allah da kuma dukan mutane.
20. Manyan firistoci da masu mulkinmu sun ba da shi a yi masa hukuncin mutuwa, suka kuwa gicciye shi.
21. Amma da, muna sa zuciya cewa, shi ne wanda zai fanshi Israʼila. Bugu da ƙari kuma yau kwana uku ke nan tun da wannan abin ya faru.
22. Har wa yau, waɗansu daga cikin matanmu sun ba mu mamaki. Sun je kabarin da sassafen nan,
23. amma ba su sami jikinsa ba. Sun dawo sun faɗa mana cewa, sun ga wahayi na malaʼiku, da suka ce yana da rai.
24. Saʼan nan, waɗansu abokanmu suka je kabarin, suka kuma tarar da kome kamar yadda matan suka faɗa, amma shi, ba su gan shi ba.”
25. Sai ya ce musu, “Ashe, ku marasa azanci ne, masu nauyin zuciya na gaskata, da dukan abin da annabawa suka faɗa!
26. Ai, dole Kiristi yǎ sha waɗannan wahalolin, kafin yǎ shiga ɗaukakarsa.
27. Sai ya fara bayyana musu daga Musa da dukan Annabawa, abin da dukan Nassi ya faɗa a kansa.”
28. Da suka yi kusa da ƙauyen da za su, sai Yesu ya yi kamar zai ci gaba.
29. Amma suka matsa masa suka ce, “Sauka wurinmu, don dare ya kusa, rana ta kusa fāɗuwa.” Sai ya sauka wurinsu.
30. Da ya zauna a tebur tare da su, sai ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya ya fara ba su.
31. Sai idanunsu suka buɗe, suka gane shi. Sai ya ɓace musu.
32. Suka tambayi juna, “Ashe, shi ya sa zukatanmu suka kuna a cikinmu, saʼad da yake magana da mu a hanya, yana bayyana mana Nassi.”
33. Suka tashi nan da nan suka koma Urushalima. A can suka sami Sha Ɗayan nan da waɗanda suke tare da su a wuri ɗaya,
34. suna cewa, “Gaskiya ne! Ubangiji ya tashi, ya kuma bayyana ga Siman”
35. Sai su biyun nan suka ba da labarin abin da ya faru a hanya, da kuma yadda suka gane Yesu yayinda ya kakkarya burodin.