English
A A A A A

Luka 23:26-56
26. Saʼad da suna tafiya da Yesu, sai wani da ake kira Siman, mutumin Sairin, yana zuwa daga ƙauye. Suka kama shi, suka aza masa gicciyen, suka tilasta shi ya ɗauki gicciyen, ya bi Yesu a baya.
27. Mutane da yawa sosai suka bi shi, a cikinsu ma da mata waɗanda suka yi makomi da kuka dominsa.
28. Yesu ya juya, ya ce musu, “ʼYan matan Urushalima, kada ku yi kuka saboda ni, amma ku yi kuka saboda kanku, da kuma saboda ʼyaʼyanku.
29. Gama lokaci yana zuwa da za ku ce, ‘Masu albarka ne bakararru, wato, mata marasa haihuwa, da mahaihuwar da ba su taɓa haihuwa ba, da kuma mama da ba su taɓa shayar da nono ba!’
30. Saʼan nan, “ ‘za su ce wa duwatsu, “Ku fāɗi a kanmu!” Za su ce wa tuddai kuma, “Ku rufe mu!” ’
31. Gama in mutane suna yin waɗannan abubuwa a lokacin da itace na ɗanye, me zai faru in ya bushe?”
32. Tare da shi akwai mutum biyu masu laifi, da aka tafi da su don a gicciye.
33. Da suka isa wurin da ake kira “Ƙoƙon Kai,” nan suka gicciye shi, tare da masu laifin nan, ɗaya a hannun damansa, ɗayan kuma a hagunsa.
34. Yesu ya ce, “Ya Uba ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba tufafinsa ta wurin jefa ƙuriʼa.
35. Mutanen suka tsaya suna ƙallo. Har masu mulki ma suka yi masa baʼa, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, to, ya ceci kansa in shi ne Kiristi na Allah, Zaɓaɓɓe.”
36. Sojoji su ma, suka zo suka yi masa baʼa. Suka miƙa masa ruwan tsami.
37. Suka ce, “In kai ne sarkin Yahudawa, ka ceci kanka mana.”
38. Bisa da shi kuma akwai wani rubutu da ya ce, “WANNAN SHI NE SARKIN YAHUDAWA.”
39. Ɗaya daga cikin masu laifin da aka gicciye a wurin ya zazzage shi, ya ce, “Shin, ba kai ne Kiristi ba? To, ka ceci kanka, ka kuma cece mu mana!”
40. Amma ɗayan mai laifi ya kwaɓe shi, ya ce, “Ba ka da tsoron Allah ne, wai saboda kana ƙarƙashin hukunci ɗaya tare da shi?
41. Horonmu, daidai aka yi mana, sakamakon abin da muka yi ne. Amma wannan mutum, bai yi wani laifi ba.”
42. Sai ya ce, “Yesu, ka tuna da ni saʼad da ka shiga mulkinka.”
43. Yesu ya amsa, ya ce masa, “Gaskiya nake faɗa maka, yau ɗin nan, za ka kasance tare da ni, a mulkina a sama.”
44. Yanzu kuwa wajen saʼa ta shida ne, kuma duhu ya rufe koʼina a ƙasar, har zuwa saʼa ta tara,
45. domin rana ta daina haskakawa. Labulen da yake cikin haikali kuma ya yage kashi biyu.
46. Yesu ya yi kira da babbar murya, ya ce, “Ya Uba, na danƙa ruhuna a hannunka.” Da ya faɗi haka, sai ya ja numfashi na ƙarshe.
47. Da jarumin ya ga abin da ya faru, sai ya yabi Allah, ya ce, “Gaskiya, wannan mutum mai adalci ne.”
48. Da dukan mutanen da suka taru, domin shaidar waɗannan abubuwa, suka ga abin da ya faru, sai suka buga ƙirjinsu suka tafi.
49. Amma dukan mutanen da suka san Yesu, tare da mata da suka bi shi daga Galili, suka tsaya daga nesa suna ƙallon abubuwan nan.
50. Akwai wani mutum mai suna Yusuf, ɗan Majalisa, wanda shi nagari ne, mai adalci,
51. shi dā ma bai yarda da shawararsu, da kuma abin da suka yi ba. Shi daga Arimateya ne wani garin Yahudiya. Yana kuma jiran zuwa mulkin Allah.
52. Sai ya je wurin Bilatus ya roƙa a ba shi jikin Yesu.
53. Sai ya saukar da jikin, ya nannaɗe shi a cikin zanen lilin, ya sa shi a wani kabari da aka fafe a cikin dutse, wadda ba a taɓa sa kowa ba.
54. An yi haka ne a Ranar Shirye-shirye, ranar Asabbaci kuma yana dab da farawa.
55. Matan da suka zo tare da Yesu, daga Galili suka bi Yusuf suka ga kabarin, da kuma yadda aka ajiye jikin.
56. Saʼan nan, suka koma gida, suka shirya kayan ƙanshi da turare. Amma suka huta a ranar Asabbaci don kiyaye doka.