English
A A A A A

Luka 23:1-25
1. Sai dukan majalisa suka tashi, suka kai shi gaban Bilatus.
2. Suka fara zarginsa suna cewa, “Mun sami wannan mutum yana rikitar da alʼummarmu. Yana hana a ba wa Kaisar haraji. Yana kuma cewa, shi Kiristi ne, sarki kuma.”
3. Sai Bilatus ya tambayi Yesu, ya ce, “Kai ne sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa, ya ce, “I, haka yake, kamar yadda ka faɗa.”
4. Sai Bilatus ya sanar wa manyan firistoci da taron, ya ce, “Ni fa, ban sami wani tushen zargi game wannan mutum nan ba.”
5. Amma suka nace, suna cewa, “Yana ta da hankulan mutane, a koʼina a Yahudiya da koyarwarsa. Ya fara daga Galili, ga shi kuma har ya kai nan.”
6. Da Bilatus ya ji haka, sai ya yi tambaya, “Ko shi mutumin Galili ne?”
7. Da ya ji cewa, Yesu yana ƙarƙashin mulkin Hiridus, sai ya aika da shi zuwa wurin Hiridus, don a lokacin kuwa Hiridus yana Urushalima.
8. Da Hiridus ya ga Yesu, sai ya yi murna ƙwarai, don tun dā ma yana marmari ya gan shi. A kan abin da ya ji game da shi, ya yi fata ya ga Yesu, ya yi waɗansu ayyukan banmamaki.
9. Ya yi masa tambayoyi masu yawa, amma Yesu bai bashi ko amsa ba.
10. Manyan firistoci da malaman dokoki suna tsaye a wurin, suna kawo zargi masu ƙarfi a kansa.
11. Sai Hiridus da sojojinsa suka wulaƙanta shi, suka yi masa baʼa. Saʼan nan, suka sa masa babban riga, suka mai da shi wurin Bilatus.
12. A ranar, Hiridus da Bilatus suka zama abokan juna, don tun dā ma, su abokan gāba ne.
13. Bilatus ya tara manyan firistoci, da masu mulki, da mutane,
14. ya ce musu, “Kun kawo mini wannan mutum, a matsayin wanda yana zuga mutane su yi tawaye. Na bincike shi a gabanku, ban ga a kan me kuka kawo kararsa ba.
15. Haka ma Hiridus, shi ya sa ya dawo da shi nan wurinmu. Kamar yadda ku ma kun gani, ba abin da mutumin nan ya yi, da ya isa mutuwa.
16. Saboda haka, zan hore shi, saʼan nan in sāke shi.”
17. (A kowace Biki, dole ya saki mutum ɗaya daga kurkuku.)
18. Suka yi ihu gaba ɗaya suka ce, “A yi gaba da wannan mutum! A sake mana Barabbas!”
19. (Barabbas yana kurkuku saboda laifin ta da hankali a birnin, da kuma don kisankai.)
20. Sai Bilatus ya sāke yin musu magana don yana so ya saki Yesu.
21. Amma sai suka ci gaba da ihu, suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!”
22. Ya sāke ce musu, sau na uku, “Don me? Wane laifi wannan mutum ya yi? Ni dai ban same shi da wani dalilin da ya isa a kashe shi ba. Saboda haka, zan sa a hore shi, saʼan nan in sāke shi.”
23. Amma suna ihu, suna nacewa, suna cewa, dole a gicciye shi, har ihunsu ya rinjaye shi.
24. Sai Bilatus ya biya bukatarsu da ya ji roƙonsu.
25. Ya saki mutumin da aka jefa a kurkuku saboda ta da hankali, da kisankai, shi wanda suka roƙa. Saʼan nan ya ba da Yesu ga nufinsu.