A A A A A

Luka 22:47-71
47. Yana cikin magana sai ga taro sun zo. Mutumin nan da ake kira Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun, shi ya bi da su. Sai ya matso kusa da Yesu don ya yi masa sumba.
48. Amma Yesu ya tambaye shi, ya ce, “Yahuda, ashe, da sumba za ka bashe Ɗan Mutum?”
49. Da masu bin Yesu suka ga abin da zai faru, sai suka ce, “Ubangiji, mu yi sara da takubanmu ne?”
50. Sai ɗayansu ya kai sara ga bawan babban firist, ya sare kunnen damansa.
51. Amma Yesu ya amsa, ya ce, “Kada a ƙara yin wannan haka!” Sai ya taɓa kunnen mutumin da aka sara, ya warkar da shi.
52. Sai Yesu ya ce wa manyan firistoci, da maʼaikatan ʼyan gadin haikali, da dattawa, waɗanda suka zo don su kama shi: “Ina jagoran wani tawaye ne, da za ku zo da takuba da sanduna?
53. Kullum ina tare da ku a filin haikali, amma ba ku kama ni ba. Amma wannan ne saʼa naku, lokacin da duhu yake mulki.”
54. Sai suka kama shi suka kai shi gidan babban firist. Bitrus ya bi su daga nesa.
55. Amma da suka hura wuta a tsakiyar harabar gidan, kowa ya zauna, sai Bitrus ya zo ya zauna tare da su.
56. Wata baiwa ta gan shi zaune kusa da wutan. Ta dube shi sosai saʼan nan, ta ce, “Ai, wannan mutum ma yana tare da shi.”
57. Amma ya yi musu, ya ce, “Mace, ni ban san shi ba!”
58. Bayan ɗan lokaci kaɗan, wani dabam ya gan shi, ya ce, “Kai ma ɗayansu ne.” Amma Bitrus ya amsa, ya ce, “Kai, ba na cikinsu!”
59. Bayan kamar saʼa ɗaya, sai wani mutum ya ce, “Ba shakka, mutumin nan ma yana tare da shi, don shi mutumin Galili ne.”
60. Bitrus ya amsa, ya ce, “Kai, ban ma san abin da kake magana a kai ba!” Yana cikin magana, sai zakara ya yi cara.
61. Ubangiji kuma ya juya ya kafa wa Bitrus ido. Sai Bitrus ya tuna da maganar da Ubangiji ya ce masa, “Kafin zakara ya yi cara yau, za ka yi mūsun sanina sau uku.”
62. Sai ya fita waje, ya yi kuka mai zafi.
63. Mutanen da suke gadin Yesu suka fara masa baʼa da duka.
64. Suka rufe masa idanu suna tambaya cewa, “Ka yi annabci! Wa ya mare ka?”
65. Suka kuma yi masa waɗansu baƙaƙen maganganu masu yawa.
66. Da gari ya waye, sai majalisar dattawa na mutane, da manyan firistoci, da malaman dokoki, suka taru wuri ɗaya. Sai aka kawo Yesu a gabansu.
67. Suka ce, “Ka faɗa mana, ko kai ne Kiristi?” Yesu ya amsa, ya ce, “Ko na gaya muku, ba za ku gaskata ni ba,
68. in kuma na yi muku tambaya ba za ku iya ba ni amsa ba.
69. Amma daga yanzu, Ɗan Mutum zai zauna a hannun dama na Allah Mai Iko.”
70. Sai dukansu suka tambaya, “Wato, kai Ɗan Allah ke nan?” Ya amma ya ce, “Kun faɗa daidai, ni ne.”
71. Sai suka ce, “Wace shaida kuma muke nema? Ai, mun ji abin da ya ce da bakinsa.”