A A A A A

Luka 22:24-46
24. Gardama ta kuma tashi a tsakaninsu, a kan ko wane ne a cikinsu ya fi girma.
25. Yesu ya ce musu, “Sarakunan Alʼummai suna nuna iko a kan mutanensu, kuma waɗanda suke nuna iko a kansu, suna kiran kansu Masu Taimakon mutane.
26. Amma ku, kada ku zama haka. A maimakon haka, sai dai wanda ya fi girma a cikinku, ya zama kamar wanda ya fi ƙanƙanta, wanda kuma ke mulki, ya zama kamar mai hidima.
27. Wane ne ya fi girma? Wanda yake zaune a tebur ne, ko kuma shi da yake yin hidima? Ashe, ba wanda yake zaune a tebur ba ne? Amma ga ni, ni mai yin hidima ne a cikinku.
28. “Ku ne kuka tsaya tare da ni a gwaje-gwajen da na sha.
29. Daidai kamar yadda Ubana ya ba ni mulki, haka ni ma nake ba ku.
30. Saboda ku ci, ku sha a teburina a cikin mulkina. Kuma ku zauna a kan gadon sarauta, ku yi wa kabilai goma sha biyu na Israʼila shariʼa.
31. “Siman, Siman, Shaiɗan ya nemi izini ya sheƙe ka kamar alkama.
32. Amma na yi maka adduʼa, Siman, domin kada bangaskiyarka ta kāsa. Bayan ka juyo, ka ƙarfafa ʼyanʼuwanka.”
33. Amma ya amsa, ya ce, “Ubangiji, ina a shirye in tafi tare da kai har kurkuku, ko mutuwa ma.”
34. Yesu ya ce, “Ina gaya maka Bitrus, kafin zakara ya yi cara yau, za ka yi mūsun sanina sau uku.”
35. Sai Yesu ya tambaye, su ya ce, “Lokacin da na aike ku ba tare da jakar kuɗi, ko jaka, ko takalma ba, kun rasa wani abu?” Suka amsa, “Babu.”
36. Ya ce musu, “Amma yanzu, in kuna da jakar kuɗi, ko jaka, ku ɗauka. In kuma ba ku da takobi, ku sayar da rigarku, ku saya.
37. A rubuce yake cewa, ‘An lissafta shi tare da masu zunubi’; ina kuwa gaya muku, dole wannan ya cika a kaina. I, abin da aka rubuta a kaina yana kusan cikawa.”
38. Almajiran suka ce, “Duba Ubangiji, ga takuba biyu.” Yesu ya ce, “Ya isa.”
39. Yesu ya fita zuwa Dutsen Zaitun kamar yadda ya saba, almajiransa kuma suka bi shi.
40. Da ya kai wurin, sai ya ce musu, “Ku yi adduʼa don kada ku fāɗi cikin jaraba.”
41. Sai ya janye daga wurinsu, misalin nisan jifa, ya durƙusa a ƙasa ya yi adduʼa,
42. “Uba, in ka yarda, ka ɗauke mini wannan kwaf, amma ba nufi na ba, sai dai naka.”
43. Wani malaʼika daga sama ya bayyana gare shi, ya ƙarfafa shi.
44. Domin tsananin azaba, sai ya ƙara himma cikin adduʼa, zufansa kuma na ɗigowa ƙasa kamar jini.
45. Da ya tashi daga adduʼa, ya koma inda almajiransa suke, sai ya iske su suna barci, daga gajiyar baƙin ciki.
46. Ya tambaye su, “Don me kuke barci? Ku tashi ku yi adduʼa, don kada ku fāɗi cikin jaraba.”