A A A A A

Yohanna 11:30-56
30. Yesu dai bai riga ya shiga ƙauyen ba tukuna, har yanzu yana inda Marta ta tarye shi.
31. Da Yahudawan da suke tare da Maryamu a cikin gida, suke mata taʼaziyya, suka ga ta yi wuf ta fita, sai suka bi ta, suna tsammani za ta kabarin ne ta yi kuka a can.
32. Saʼad da Maryamu ta kai inda Yesu yake, ta kuma gan shi, sai ta fāɗi a gabansa ta ce, “Ubangiji, da kana nan, da ɗanʼuwana bai mutu ba.”
33. Da Yesu ya ga tana kuka, Yahudawan da suka zo tare da ita ma suna kuka, sai ya yi juyayi ƙwarai a ruhu ya kuma damu.
34. Sai ya yi tambaya, ya ce, “Ina kuka sa shi?” Suka amsa suka ce, “Ubangiji zo ka gani.”
35. Yesu ya yi kuka.
36. Sai Yahudawa suka ce, “Dubi yadda yake ƙaunarsa!”
37. Amma waɗansunsu suka ce, “Anya, wanda ya buɗe wa makahon nan idanu, ba zai iya yin wani abu yǎ hana wannan mutum mutuwa ba?”
38. Yesu, har yanzu cike da juyayi, ya zo kabarin. Kogo ne da aka rufe bakin da dutse.
39. Sai Yesu ya ce, “Ku kawar da dutsen.” Marta, ʼyarʼuwan mamacin ta ce, “Ubangiji, yanzu, ai, zai yi wari, don yau kwanansa huɗu ke nan a can.”
40. Sai Yesu ya ce, “Ban gaya miki cewa in kin gaskata za ki ga ɗaukakar Allah ba?”
41. Saboda haka suka kawar da dutsen. Saʼan nan Yesu ya dubi sama ya ce, “Uba, na gode maka da ka saurare ni.
42. Na san kullum kakan saurare ni, na dai faɗa haka ne saboda amfanin mutanen nan da suke tsaitsaye, don su gaskata cewa kai ka aiko ni.”
43. Saʼad da ya faɗa haka, sai Yesu ya yi kira da babbar murya ya ce, “Lazarus, ka fito!”
44. Sai mamacin ya fito, hannuwansa da ƙafafunsa a ɗaure da ƙyallayen lilin, fuskarsa kuwa an naɗe da mayafi. Yesu ya ce musu, “Ku tube kayan bizo, ku bar shi yǎ tafi.”
45. Saboda haka Yahudawa da yawa da suka zo don su ziyarci Maryamu, suka kuma ga abin da Yesu ya yi, suka ba da gaskiya gare shi.
46. Amma waɗansunsu suka je wurin Farisiyawa suka gaya musu abin da Yesu ya yi.
47. Sai manyan firistoci da Farisiyawa suka kira taron Majalisa. Suka yi tambaya suna cewa, “Me muke yi ne? Ga mutumin nan yana yin abubuwan banmamaki masu yawa.
48. In fa muka ƙyale shi ya ci gaba da haka, kowa zai gaskata da shi, Romawa kuma su zo su karɓe wurinmu su kuma ƙwace ƙasarmu.”
49. Sai waninsu, mai suna Kayifas, wanda ya kasance babban firist a shekarar, ya ce, “Ku dai ba ku san kome ba!
50. Ba ku gane ba, ai, gwamma mutum ɗaya yǎ mutu saboda mutane da duk ƙasar ta hallaka.”
51. Bai faɗa haka bisa nufinsa ba, sai dai a matsayinsa na babban firist a shekarar, ya yi annabci ne cewa Yesu zai mutu saboda ƙasar Yahudawa,
52. ba don ƙasan nan kaɗai ba amma don yǎ tattaro ʼyaʼyan Allah da suke warwatse ma, su zama ɗaya.
53. Saboda haka, daga wannan rana suka ƙulla su ɗauke ransa.
54. Saboda haka Yesu bai ƙara tafiya a cikin Yahudawa a sarari ba. A maimako haka sai ya janye zuwa yankin kusa da hamada, a wani ƙauye da ake kira Efraim, inda ya zauna da almajiransa.
55. Saʼad da lokaci ya yi kusa a yi Bikin Ƙetarewa na Yahudawa, da yawa suka haura daga ƙauyuka zuwa Urushalima, don su tsarkake kansu kafin Bikin Ƙetarewa.
56. Suka yi ta neman Yesu, da suke a tsaitsaye a filin haikali kuwa suka dinga tambayar juna, suna cewa, “Me kuka gani? Anya, zai zo Bikin kuwa?”