A A A A A

Yohanna 11:1-29
1. To, an yi wani mutum mai suna Lazarus wanda ya yi rashin lafiya. Shi daga Betani ne, ƙauyen su Maryamu da ʼyarʼuwarta Marta.
2. Maryamun nan kuwa, wadda ɗanʼuwanta Lazarus yake rashin lafiya, ita ce ta zuba wa Ubangiji turare ta kuma goge ƙafafunsa da gashin kanta.
3. Saboda haka ʼyanʼuwansa mata suka aika da saƙo wa Yesu cewa, “Ubangiji, ga wanda kake ƙauna yana rashin lafiya.”
4. Saʼad da ya ji haka, sai Yesu ya ce, “Wannan rashin lafiya ba zai kai ga mutuwa ba. Aʼa, sai dai don a ɗaukaka Allah a kuma ɗaukaka Ɗan Allah ta wurin wannan.”
5. Yesu kuwa yana ƙaunar Marta da ʼyarʼuwarta da kuma Lazarus.
6. Duk da haka saʼad da ya ji Lazarus ba shi da lafiya, sai ya ƙara kwana biyu a inda yake.
7. Sai ya ce wa almajiransa, “Mu koma Yahudiya.”
8. Sai suka ce, “Rabbi, ba da daɗewa ba ne Yahudawa suka nemi su jajjefe ka, duk da haka za ka koma can?”
9. Yesu ya amsa, ya ce, “Ba saʼa goma sha biyu ce yini guda ba? Mutumin da yake tafiya da rana ba zai yi tuntuɓe ba domin yana ganin hasken duniyan nan.
10. Sai a saʼad da yake tafiya da dare ne zai yi tuntuɓe, don ba shi da haske.”
11. Bayan ya faɗa haka, sai ya ƙara ce musu, “Abokinmu Lazarus ya yi barci, amma za ni in tashe shi.”
12. Almajiransa suka ce, “Ubangiji, in barci ne yake, to, ai, zai sami sauƙi.”
13. Yesu kuwa yana magana mutuwarsa ce, amma almajiransa suka ɗauka yana nufin barcin gaskiya ne.
14. Saboda haka sai ya gaya musu a fili cewa, “Lazarus ya mutu,
15. amma saboda ku na yi farin ciki da ba na can, domin ku gaskata. Amma mu dai je wurinsa.”
16. Sai Toma (wanda ake kira Didaimus) ya ce wa sauran almajiran, “Mu ma mu je, mu mutu tare da shi.”
17. Da isowarsa, Yesu ya tarar Lazarus ya riga ya yi kwana huɗu a kabari.
18. Betani bai kai mil biyu ba daga Urushalima,
19. Yahudawa da yawa kuwa suka zo wurin Marta da Maryamu don su yi musu taʼaziyya, saboda rasuwar ɗanʼuwansu.
20. Saʼad da Marta ta ji cewa Yesu yana zuwa, sai ta fita don ta tarye shi, amma Maryamu ta zauna a gida.
21. Sai Marta ta ce wa Yesu, “Ubangiji, da kana nan da ɗanʼuwana bai mutu ba.
22. Amma na san cewa ko yanzu ma Allah zai ba ka duk abin da ka roƙa.”
23. Yesu ya ce mata, “Ɗanʼuwanki zai sāke tashi.”
24. Marta ta amsa ta ce, “Na sani zai sāke tashi a tashin matattu a rana ta ƙarshe.”
25. Yesu ya ce mata, “Ni ne tashin matattu da kuma rai. Duk wanda ya gaskata da ni zai rayu, ko ya mutu;
26. kuma duk wanda yake raye ya kuma gaskata da ni ba zai taɓa mutuwa ba. Kin gaskata wannan?”
27. Sai ta ce masa, “I, Ubangiji, na gaskata kai ne Kiristi, Ɗan Allah, mai zuwa cikin duniya.”
28. Bayan ta faɗa haka kuwa, sai ta koma ta je ta kira ʼyarʼuwarta Maryamu a gefe. Ta ce, “Ga Malam ya zo, kuma yana kiranki.”
29. Saʼad da Maryamu ta ji haka sai ta yi wuf ta tafi wurinsa.