A A A A A

Luka 22:1-23
1. Yanzu fa, Bikin Burodi Marar Yistin da ake kira Bikin Ƙetarewa ya yi kusa,
2. manyan firistoci da malaman dokoki kuma suna neman yadda za su kashe Yesu a ɓoye, don suna tsoron mutane.
3. Shaiɗan kuwa ya shiga cikin zuciyar Yahuda, wanda ake kira Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun.
4. Sai Yahuda ya je ya tattauna da manyan firistoci, da maʼaikatan ʼyan gadin haikali, a kan yadda zai ba da Yesu a gare su.
5. Suka kuwa yi murna, suka yarda su ba shi kuɗi.
6. Ya ko yarda, ya fara neman zarafin da zai ba da Yesu a gare su, saʼad da taro ba sa nan tare da shi.
7. Sai ranar Bikin Burodi Marar Yisti ya zo, wato, ranar hadayar ɗan ragon kafara na Bikin Ƙetarewa.
8. Sai Yesu ya aiki Bitrus da Yohanna, ya ce musu, “Ku je ku yi shirye-shiryen Bikin Ƙetarewa da za mu ci.”
9. Suka tambaye shi suka ce, “Ina kake so mu yi shirin?”
10. Ya amma ya ce, “Saʼad da kuka shiga cikin birnin, za ku sadu da wani mutum yana ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi zuwa gidan da zai shiga.
11. Ku ce wa maigidan, Malam ya aike mu mu ce maka, ‘Ina ɗakin baƙi, inda ni da almajiraina za mu ci abincin Bikin Ƙetarewa?’
12. Zai nuna muku wani babban ɗakin sama a shirye. Nan za ku yi shirin.”
13. Sai suka tafi, suka kuma iske kome kamar yadda Yesu ya faɗa musu. Sai suka shirya Bikin Ƙetarewa.
14. Da lokaci ya yi, sai Yesu ya zauna tare da manzanninsa a tebur.
15. Sai ya ce musu, “Na yi marmari ƙwarai don in ci wannan Bikin Ƙetarewa tare da ku, kafin in sha wahala.
16. Ina dai gaya muku, ba zan ƙara cin sa ba, sai ya sami cika a mulkin Allah.”
17. Bayan ya ɗauki kwaf ruwan inabi, ya yi godiya, sai ya ce, “Ku karɓa, ku rarraba wa junanku.
18. Ina dai gaya muku, ba zan ƙara sha daga ʼyaʼyan inabi ba, sai mulkin Allah ya zo.”
19. Sai ya ɗauki burodi ya yi godiya, ya kakkarya ya ba su, da cewa: “Wannan jikina ne, da aka bayar dominku. Ku riƙa yin haka don tunawa da ni.”
20. Haka kuma, bayan abincin, ya ɗauki kwaf ruwan inabi, ya ce, “Wannan kwaf ruwan inabi shi ne, na sabon alkawari cikin jinina, da aka zubar dominku.
21. “Amma hannun wanda zai ci amanata, yana cin abincin tare da ni.
22. Ɗan Mutum zai mutu kamar yadda aka ƙaddara, amma kaiton mutumin da zai bashe shi.”
23. Sai suka fara tambayar junansu, ko wane ne a cikinsu zai yi wannan.