English
A A A A A

Yohanna 10:24-42
24. Yahudawa suka taru kewaye da shi, suna cewa, “Har yaushe za ka bar mu cikin shakka? In kai ne Kiristi ka faɗa mana a fili mana.”
25. Yesu ya amsa, ya ce, “Na faɗa muku, amma ba ku gaskata ba. Ayyukan banmamakin da nake yi cikin sunan Ubana suna shaida ni,
26. amma ba ku gaskata ba domin ku ba tumakina ba ne.
27. Tumakina sukan saurari muryata; na sansu, suna kuma bi na.
28. Ina ba su rai madawwami, ba za su taɓa hallaka ba; ba kuma mai ƙwace su daga hannuna.
29. Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi duka girma, ba mai ƙwace su daga hannun Ubana.
30. Da ni da Uba ɗaya ne.”
31. Sai Yahudawa suka sāke ɗebo duwatsu don su jajjefe shi,
32. amma Yesu ya ce musu, “Na nuna muku manyan ayyukan banmamaki daga wurin Uba. A kan wanne a cikinsu kuke so ku jajjefe ni?”
33. Sai Yahudawa suka ce, “Ba don wani daga cikin waɗannan muke so mu jajjefe ka ba, sai don saɓo, kai da kake mutum kawai, kana mai da kanka Allah.”
34. Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba a rubuce yake a cikin Dokarku ba cewa, ‘Na ce ku alloli ne’?
35. In har ya kira su ‘alloli’, waɗanda maganar Allah ta zo musu-Nassi ba zai karyuwa ba— 
36. me za ku ce game da wanda Allah ya keɓe wa kansa ya kuma aiko duniya? Don me kuke zargi na a kan saɓo, don na ce, ‘Ni Ɗan Allah ne?’
37. Kada ku gaskata da ni in ba abin da Ubana yake yi ne nake yi ba.
38. Amma in ina yinsu, ko ba ku gaskata da ni ba, ku gaskata da ayyukan banmamakin, don ku sani ku kuma gane cewa, Uba yana a cikina, ni kuma ina a cikin Uba.”
39. Sai suka sāke yin ƙoƙarin su kama shi, amma ya kuɓuce musu.
40. Saʼan nan Yesu ya sāke koma ƙetaren Urdun inda dā Yohanna yake baftisma. A can ya zauna
41. mutane da yawa suka zo wurinsa. Suka ce, “Ko da yake Yohanna bai yi waata abin banmamaki ba, duk abubuwan da Yohanna ya faɗa game da mutumin nan gaskiya ne.”
42. A nan kuwa mutane da yawa suka gaskata da Yesu.