A A A A A

Yohanna 10:1-23
1. “Gaskiya nake gaya muku, mutumin da bai shiga wurin kwanan garken tumaki ta ƙofa ba, amma ya hau ta wata hanya dabam, ɓarawo ne ɗan fashi kuma.
2. Mutumin da ya shiga ta ƙofa makiyayin tumakinsa ne.
3. Mai gadin yakan buɗe masa ƙofa, tumakin kuma sukan saurari muryarsa. Yakan kira tumakinsa da suna yǎ kuma fid da su waje.
4. Saʼad da ya fitar da dukan nasa a waje, sai ya ja gabansu, tumakinsa kuma sukan bi shi domin sun san muryarsa.
5. Amma ba za su taɓa bin baƙo ba; sai dai su guje shi domin ba su san muryar baƙo ba.”
6. Yesu ya yi wannan karin maganar, amma ba su fahimci abin da yake faɗa musu ba.
7. Saboda haka Yesu ya sāke cewa, “Gaskiya nake gaya muku, ni ne ƙofar tumakin.
8. Duk waɗanda suka riga ni zuwa ɓarayi ne, ʼyan fashi kuma, amma tumakin ba su saurare su ba.
9. Ni ne ƙofar; duk wanda ya shiga ta wurina zai sami ceto. Zai riƙa shiga yǎ fita yǎ kuwa sami wurin kiwo.
10. Ɓarawo yakan zo don yǎ yi sata ne kawai da kisa da kuma ɓarna. Ni kuwa na zo ne don su sami rai, su kuma same shi a yalwace.
11. “Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yakan ba da ransa domin tumakin.
12. Wanda aka ɗauko haya ba shi ne makiyayi mai tumakin ba. Saboda haka saʼad da ya ga kyarkeci yana zuwa, sai yǎ sheƙa da gudu yǎ bar tumakin. Sai kyarkecin yǎ kai wa garken hari, yǎ kuma watsar da su.
13. Mutumin yakan gudu don shi ɗan haya ne kawai, bai kuwa damu da tumakin ba.
14. “Ni ne makiyayi mai kyau; na san tumakina, tumakina kuma sun san ni— 
15. kamar yadda Uba ya san ni, ni kuma na san Uba-ina kuwa ba da raina domin tumakin.
16. Ina kuma da waɗansu tumakin da ba na wannan garken ba ne. Dole ne in kawo su. Su ma za su saurari muryata, za su kasance garke guda ɗaya da kuma makiyayi guda.
17. Abin da ya sa Ubana yake ƙaunata shi ne, domin ina ba da raina-in kuma ɗauko shi.
18. Ba mai ƙwace mini shi, sai dai don kaina nake ba da shi. Ina da iko in ba da shi, ina da iko in ɗauko shi kuma. Wannan umarni kuwa daga wurin Ubana ne na karɓo.”
19. Saboda waɗannan kalmomi fa, Yahudawa suka sāke samun baraka a cikinsu.
20. Da yawa daga cikinsu suka ce, “Yana da aljani yana kuma hauka. Don me za ku saurare shi?”
21. Amma waɗansu suka ce, “Kai, waɗannan kalmomi ba na mai aljani ba ne. Aljani yana iya buɗe idanun makaho?”
22. Sai lokacin Bikin Miƙawa a Urushalima ya kewayo. Lokacin sanyin hunturu ne,
23. Yesu kuwa yana a filin haikali yana zagawa a Shirayin Solomon.