English
A A A A A

Yohanna 9:24-41
24. Sai suka sāke kiran mutumin nan da yake makaho a dā, suka ce masa, “Ka ɗaukaka Allah, mu kam, mun san mutumin nan mai zunubi ne.”
25. Sai ya amsa, ya ce, “Ko shi mai zunubi ne ko babu, ni dai ban sani ba. Abu ɗaya fa na sani, dā ni makaho ne, amma yanzu ina gani!”
26. Sai suka tambaye suka ce, “Shin, me ya yi maka? Ta yaya ya buɗe idanunka?”
27. Ya amsa ya ce, “Na riga na gaya muku ba ku kuwa saurara ba. Don me kuke so ku sāke ji? Ko ku ma kuna so ku zama almajiransa ne?”
28. Sai suka hau shi da zagi suna cewa, “Kai ne dai almajirin mutumin! Mu almajiran Musa ne!
29. Mun dai san cewa Allah ya yi magana da Musa, amma wannan mutum ba mu san inda ya fito ba.”
30. Sai mutumin ya ce, “Cab, yau ga abin mamaki! Ba ku san inda ya fito ba, ga shi kuwa ya buɗe idanuna.
31. Mun san cewa Allah ba ya sauraron masu zunubi. Yakan saurari mai tsoronsa mai aikata nufinsa.
32. Ba wanda ya taɓa ji cewa an buɗe idanun wanda aka haifa makaho.
33. Da mutumin nan ba daga Allah ba ne, da ba abin da zai iya yi.”
34. Sai suka amsa suka ce, “Kai da aka haifa cike da zunubi; za ka yi karambanin koyarwar da mu!” Sai suka kore shi.
35. Yesu ya ji labari cewa sun kore shi, da ya same shi kuwa, sai ya ce, “Ka gaskata da Ɗan Mutum?”
36. Sai mutumin ya amsa, ya ce, “Ranka yǎ daɗe, wane ne shi? Gaya mini, don in gaskata da shi.”
37. Yesu ya ce, “Yanzu ka gan shi; tabbatacce ma, shi ne yake magana da kai.”
38. Sai mutumin ya ce, “Ubangiji, na gaskata,” ya kuma yi masa sujada.
39. Yesu ya ce, “Saboda shariʼa ce na zo duniya nan, saboda makafi su sami ganin gari, waɗanda suke gani kuma su makance.”
40. Da Farisiyawan da suke tare da shi suka ji ya faɗi haka sai suka yi tambaya suka ce, “Mene? Mu ma makafi ne?”
41. Yesu ya ce, “Ai, da ku makafi ne ma, da ba ku da zunubi, amma da yake kun ce, kuna gani, zunubanku suna nan daram.