A A A A A

Yohanna 9:1-23
1. Da yana tafiya, sai ya ga wani mutum wanda aka haifa makaho.
2. Sai almajiransa suka tambaye shi suka ce, “Rabbi, wane ne ya yi zunubi, mutumin ne, ko iyayensa, da ya sa aka haife shi makaho?”
3. Sai Yesu ya ce, “Ba don mutumin ko iyayensa sun yi zunubi ne ba, sai dai don a bayyana aikin Allah ne a rayuwarsa.
4. Muddin da sauran rana, dole mu yi aikin wanda ya aiko ni. Dare yana zuwa, saʼad da ba wanda zai iya yin aiki.
5. Yayinda ina a cikin duniya, ni ne hasken duniya.”
6. Bayan ya faɗi haka, sai ya tofa miyau a ƙasa, ya kwaɓa laka da miyau ɗin, ya kuma shafa a idanun mutumin.
7. Ya ce masa, “Je ka, ka wanke a Tafkin Silowam” (kalman nan tana nufin Aikakke). Saboda haka mutumin ya tafi ya wanke, ya kuma dawo gida yana gani.
8. Maƙwabta da waɗanda suka saba ganinsa dā yana bara, suka ce, “Kai, ba wannan mutum ne ya saba zama yana bara ba?”
9. Waɗansu suka ce shi mana. Waɗansu kuwa suka ce, “Aʼa, ya dai yi kama da shi.” Amma shi ɗin ya ce, “Ƙwarai kuwa ni ne.”
10. Sai suka ce, “To, yaya aka yi idanunka suka buɗe?”
11. Ya amsa ya ce, “Mutumin da ake kira Yesu ne ya kwaɓa laka ya shafa mini a idanu. Ya ce mini in je Silowam in wanke. Na kuwa tafi, na wanke, sai na sami ganin gari.”
12. Suka tambaye shi suka ce, “Ina mutumin yake?” Ya ce, “Ban sani ba.”
13. Sai suka kawo mutumin da dā yake makaho wurin Farisiyawa.
14. To, a ranar da Yesu ya kwaɓa laka ya buɗe idanun mutumin ranar Asabbaci ce.
15. Saboda haka Farisiyawa suka tambaye shi yadda ya sami ganin gari. Mutumin ya amsa, “Ya shafa laka a idanuna, sai na wanke, ina kuwa gani.”
16. Sai waɗansu daga cikin Farisiyawa suka ce, “Mutumin nan ba daga Allah yake ba, don ba ya kiyaye ranar Asabbaci.” Amma waɗansu suka yi tambaya suka ce, “Yaya mutum mai zunubi zai yi irin abubuwan banmamaki haka?” Sai raʼayinsu ya sha bamban.
17. A ƙarshe suka sāke koma ga makahon suka ce, “Kai fa, me ka gani game da shi? Idanunka ne fa ya buɗe.” Sai mutumin ya ce, “Tab, ai, shi annabi ne.”
18. Yahudawa dai ba su yarda cewa dā shi makaho ne ya kuma sami ganin gari ba, sai da suka kira iyayen mutumin.
19. Suka tambaye su, “Wannan ɗanku ne? Shi ne wanda kuka ce an haife shi makaho? To, ta yaya yake gani yanzu?”
20. Iyayen suka amsa suka ce, “Mun dai san shi ɗanmu ne, mun kuma san cewa an haife shi makaho.
21. Sai dai yadda yake gani yanzu, ko kuma wa ya buɗe idanunsa, ba mu sani ba. Ku tambaye shi. Ai, shi ba yaro ba ne, zai faɗa da bakinsa.”
22. Iyayensa sun faɗa haka ne saboda suna tsoron Yahudawa, gama Yahudawa sun riga sun yanke shawara cewa duk wanda ya yarda cewa Yesu shi ne Kiristi, za a kore da shi daga majamiʼa.
23. Shi ya sa iyayensa suka ce, “Ai, shi ba yaro ba ne, ku tambaye shi.”