A A A A A

Yohanna 8:28-59
28. Saboda haka Yesu ya ce, “Saʼad da kuka ɗaga Ɗan Mutum, a saʼan nan ne za ku san cewa ni ne wannan da na ce nake. Ni kuwa ba na yin kome ni kaɗai, sai in dai faɗi abin da Uba ya koya mini.
29. Wanda kuwa ya aiko ni yana tare da ni; bai bar ni ni kaɗai ba, domin kullum ina aikata abin da ya gamshe shi.”
30. Saʼad da yake cikin magana, da yawa suka ba da gaskiya gare shi.
31. Sai Yesu ya ce wa Yahudawan da suka gaskata da shi, “In dai kun riƙe koyarwata, ku almajiraina ne da gaske.
32. Saʼan nan za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za ta ʼyantar da ku.”
33. Sai suka amsa masa suka ce, “Ai, mu zuriyar Ibrahim ne kuma ba mu taɓa bauta wa kowa ba. Yaya za ka ce za a ʼyantar da mu?”
34. Yesu ya amsa, ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, duk mai yin zunubi bawan zunubi ne.
35. Bawa dai ba shi da wurin zama na ɗin ɗin ɗin a cikin iyali, amma ɗa na gida ne har abada.
36. Saboda haka in Ɗan ya ʼyantar da ku, za ku ʼyantu da gaske.
37. Na dai san ku zuriyar Ibrahim ne. Duk da haka kuna shiri ku kashe ni, don maganata ba ta da wurin zama a cikinku.
38. Ina faɗi muku abin da na gani a wurin Ubana, ku kuwa kuna yin abin da kuka ji daga wurin ubanku.”
39. Suka ce, “To, ai, Ibrahim ne mahaifinmu.” Yesu ya ce, “Da ku ʼyaʼyan Ibrahim ne, da za ku aikata abubuwan da Ibrahim ya yi.
40. Ga shi kun ƙudura, sai kun kashe ni, ni mutumin da ya faɗa muku gaskiyar da na ji daga Allah. Ibrahim bai yi irin waɗannan abubuwa ba.
41. Kuna yin abubuwan da ubanku yake yi ne.” Suka ce, “Mu fa ba shegu ba ne. Uba guda kaɗai da muke da shi, shi ne Allah kansa.”
42. Yesu ya ce musu, “Da Allah ne Ubanku, da kun ƙaunace ni, gama daga Allah na fito yanzu kuma ga ni nan. Ban zo saboda kaina ba, amma shi ne ya aiko ni.
43. Me ya sa ba kwa gane da maganata? Don ba kwa iya jin abin da nake faɗi.
44. Ku na ubanku ne, Iblis, kuna kuwa so ku aikata abin da ubanku yake so. Shi mai kisankai ne tun farko. Ba ya ruwansa da gaskiya, gama gaskiya ba ta cikinsa. Yayinda yake ƙarya, yana yin halinsa ne, gama shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma.
45. Amma domin ina faɗin gaskiya, ba kwa gaskata!
46. Akwai waninku da zai iya haƙaƙƙewa na taɓa yin zunubi? In kuwa gaskiya na faɗa, me ya sa ba kwa gaskata ni?
47. Wanda yake na Allah, yakan ji abin da Allah yake faɗi. Abin da ya sa ba kwa jinsa kuwa shi ne don ku ba na Allah ba ne.”
48. Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Aha, ai, gaskiyarmu da muka ce kai mutumin Samariya ne, kana kuma da aljani.”
49. Yesu ya ce, “Ni ba mai aljani ba ne, ni dai ina girmama Ubana, ku kuwa ba kwa girmama ni.
50. Ba na nema wa kaina ɗaukaka, amma akwai wani wanda yake neman mini, shi ne kuma alƙali.
51. Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya kiyaye maganata, ba zai ɗanɗana mutuwa ba sam.”
52. Da jin haka Yahudawa suka ce, “Tabɗi, yanzu kam mun san kana da aljani! Ibrahim ya mutu haka ma annabawa, ga shi kana cewa duk wanda ya kiyaye maganarka ba zai ɗanɗana mutuwa ba sam.
53. Ka fi Ibrahim mahaifinmu ne? Ya mutu, haka ma annabawa. Wa kake ɗauka kanka ne?”
54. Yesu ya amsa, ya ce, “In ma na ɗaukaka kaina, ɗaukakata ba kome ba ce. Ubana, wanda kuke cewa shi ne Allahnku, shi ne wanda yake ɗaukaka ni.
55. Ko da yake ba ku san shi ba, ni dai na san shi. In kuwa na ce ban san shi ba, na zama maƙaryaci kamarku ke nan, amma na san shi, kuma ina kiyaye maganarsa.
56. Mahaifinku Ibrahim ya yi farin ciki sosai yǎ sami ganin ranata; ya kuwa gan ta, ya yi murna.”
57. Sai Yahudawa suka ce masa, “Kai, shekarunka har yanzu ba su kai hamsin ba tukuna, har ka ga Ibrahim!”
58. Yesu ya amsa, ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, tun ba a haifi Ibrahim ba, Ni ne!”
59. Da jin haka sai suka ɗebo duwatsu don su jajjefe shi, amma Yesu ya ɓuya, ya fita daga filin haikali.