A A A A A

Yohanna 8:1-27
1. Amma Yesu ya tafi Dutsen Zaitun.
2. Da sassafe ya sāke bayyana a filin haikali, inda dukan mutane suka taru kewaye da shi, sai ya zauna don yǎ koya musu.
3. Sai malaman dokoki da Farisiyawa suka kawo wata macen da aka kama a zina. Suka sa ta tsaya a gaban taron
4. suka kuma ce wa Yesu, “Malam, an kama wannan mace tana zina.
5. A cikin Doka Musa ya umarce mu, mu jajjefe irin waɗannan mata. To, me ka ce?”
6. Sun yi wannan tambaya ce don su sa masa tarko, don su sami hanyar zarge shi. Amma Yesu ya sunkuya ya fara rubutu a ƙasa da yatsarsa.
7. Da suka ci gaba da yin masa tambayoyi, sai ya miƙe tsaye ya ce musu, “In da wani a cikinku da ba shi da zunubi, sai yǎ fara jifanta da dutse.”
8. Sai ya sāke sunkuyawa ya kuma yi rubutu a ƙasa.
9. Da jin haka, waɗanda suka ji sai suka fara tashi daga wurin ɗaya-ɗaya. Manyan da farko, har sai da aka bar Yesu kaɗai, tare da macen tsaye a wurin.
10. Sai Yesu ya miƙe tsaye ya tambaye ta, “Mace, ina suke? Ba wanda ya hukunta ki?”
11. Ta ce, “Ba kowa, ranka yǎ daɗe.” Sai Yesu ya ce, “Haka ni ma ban hukunta ki ba. Ki tafi, ki daina rayuwar zunubi.”
12. Saʼad da Yesu ya sāke magana da mutanen, sai ya ce, “Ni ne hasken duniya. Duk wanda ya bi ni ba zai yi tafiya cikin duhu ba, sai dai yǎ sami hasken rayuwa.”
13. Sai Farisiyawa suka tambaye shi suka ce, “Ga kai dai, kana yi wa kanka shaida, shaidarka kuwa ba tabbatacciya ba ce.”
14. Sai Yesu ya amsa, ya ce, “Ko na shaidi kaina, ai, shaidata tabbatacciya ce, gama na san inda na fito da kuma inda za ni. Amma ku ba ku san inda na fito ko inda za ni ba.
15. Kuna shariʼa bisa ga maʼaunin mutane; ni kuwa ba na yin wa kowa shariʼa.
16. Amma ko da zan yi shariʼa, shariʼata daidai ce, don ba ni kaɗai ba ne. Ina tare da Uba da ya aiko ni.
17. A cikin Dokarku a rubuce yake cewa shaidar mutum biyu tabbatacciya ce.
18. Ni ne nake shaidar kaina, Uba da ya aiko ni kuma yana shaidata.”
19. Suka tambaye shi suka ce, “Ina Uban nan naka?” Sai Yesu ya ce, “Ba ku san ni ko Ubana ba. Da kun san ni, da za ku san Ubana ma.”
20. Ya faɗi waɗannan kalmomi ne yayinda yake koyarwa a filin haikali, kusa da inda ake ajiye baye-baye. Duk da haka ba wanda ya kama shi, domin lokacinsa bai yi ba tukuna.
21. Har wa yau Yesu ya sāke ce musu, “Zan tafi, za ku kuwa neme ni, za ku kuma mutu cikin zunubinku. Inda za ni, ba za ku iya zuwa ba.”
22. Wannan ya sa Yahudawa suka yi tambaya suka ce, “Zai kashe kansa ne? Shi ya sa yake cewa, ‘Inda za ni, ba za ku iya zuwa ba’?”
23. Amma ya ci gaba da cewa, “Ku daga ƙasa kuke; ni kuwa daga bisa ne. Ku na duniyan nan ne; ni kuwa ba na duniyan nan ba ne.
24. Na gaya muku cewa za ku mutu cikin zunubanku; in ba ku gaskata cewa ni ne wanda na ce nake ba, lalle za ku mutu cikin zunubanku.”
25. Suka ce, “Wane ne kai?” Sai Yesu ya amsa, ya ce, “Ni ne wannan da na sha faɗi muku.
26. Ina da abubuwa masu yawa da zan faɗa game ku in kuma yi muku shariʼa. Amma wanda ya aiko ni mai aminci ne, abin da kuma na ji daga gare shi, shi nake gaya wa duniya.”
27. Ba su gane cewa yana yin musu magana game da Ubansa ba ne.