A A A A A

Yohanna 7:28-53
28. Yesu yana cikin koyarwa a filin haikali ke nan, sai ya ɗaga murya ya ce, “I, kun san ni, kun kuma san inda na fito. Ban zo don kaina ba, sai dai shi da ya aiko ni mai gaskiya ne. Ba ku san shi ba,
29. amma na san shi, domin ni daga wurinsa ne, kuma shi ya aiko ni.”
30. Da jin haka, sai suka yi ƙoƙari su kama shi, sai dai ba wanda ya taɓa shi, don lokacinsa bai yi ba tukuna.
31. Duk da haka, da yawa a cikin taron suka ba da gaskiya gare shi. Suka ce, “Saʼad da Kiristi ya zo, zai yi abubuwan banmamaki fiye da na wannan mutum ne?”
32. Farisiyawa suka ji taron suna raɗe-raɗen waɗannan abubuwa game da shi. Sai manyan firistoci da Farisiyawa suka aiki masu gadin haikalin su kama shi.
33. Sai Yesu ya ce, “Ina tare da ku na ɗan ƙanƙanin lokaci ne kawai, saʼan nan zan koma wurin wanda ya aiko ni.
34. Za ku neme ni, amma ba za ku same ni ba; inda nake kuwa, ba za ku iya zuwa ba.”
35. Sai Yahudawa suka ce wa juna, “Ina mutumin nan yake niyyar tafiya da ba za mu iya samunsa ba? Zai je wurin mutanenmu da suke zaune warwatse a cikin Helenawa, yǎ kuma koya wa Helenawa ne?”
36. Me yake nufi da ya ce, “Za ku neme ni, amma ba za ku same ni ba,” da kuma “Inda nake, ba za ku iya zuwa ba?”
37. A rana ta ƙarshe kuma mafi girma ta Bikin, Yesu ya tsaya ya yi magana da babbar murya ya ce, “Duk mai jin ƙishirwa, yǎ zo wurina yǎ sha.
38. Duk wanda ya gaskata da ni, kamar yadda Nassi ya ce, kogunan ruwa masu rai za su gudana daga cikinsa.”
39. Da wannan yana nufin Ruhu ke nan, wanda waɗanda suka gaskata da shi za su karɓa daga baya. Har yǎ zuwa wannan lokaci ba a ba da Ruhu ba tukuna, da yake ba a riga an ɗaukaka Yesu ba.
40. Da jin kalmominsa, waɗansu mutane suka ce, “Ba shakka, mutumin nan shi ne Annabin.”
41. Waɗansu suka ce, “Shi ne Kiristi.” Waɗansu har wa yau suka ce, “Yaya Kiristi zai fito daga Galili?
42. Nassi bai ce Kiristi zai fito daga zuriyar Dawuda, daga kuma Betlehem garin da Dawuda ya zauna ba?”
43. Sai mutanen suka rabu saboda Yesu.
44. Waɗansu suka so su kama shi, sai dai ba wanda ya taɓa shi.
45. A ƙarshe masu gadin haikali suka koma wurin manyan firistocin da Farisiyawa, waɗanda suka tambaye su cewa, “Don me ba ku kawo shi nan ba?”
46. Sai masu gadin suka ce, “Kai, babu wanda ya taɓa magana kamar wannan mutum.”
47. Sai Farisiyawa suka amsa cikin fushi suka ce, “Af, kuna nufi har da ku ma ya ruɗe ku ke nan?
48. Akwai wani daga cikin masu mulki ko cikin Farisiyawan da ya gaskata da shi?
49. Aʼa! Sai dai wannan taron da ba su san kome game da Doka ba-laʼanannu ne.”
50. Nikodimus, wanda ya je wurin Yesu dā, wanda kuma yake ɗayansu ya ce,
51. “Ashe, dokarmu takan hukunta mutum ba tare da an fara ji daga bakinsa game da abin da yake yi ba?”
52. Sai suka amsa suka ce, “Kai ma daga Galili ne? Bincika ka gani, za ka iske cewa ba annabin da zai fito daga Galili.”
53. Sai kowannensu ya koma gidansa.