English
A A A A A

Yohanna 7:1-27
1. Bayan wannan, sai Yesu ya yi ta zagawa a cikin Galili, da ganga bai yarda yǎ je Yahudiya ba domin Yahudawa a can suna nema su kashe shi.
2. Amma saʼad da Bikin Bukkokin Yahudawa ya yi kusa,
3. sai ʼyanʼuwan Yesu suka ce masa, “Ya kamata ka bar nan ka tafi Yahudiya, don almajiranka su ga ayyukan banmamaki da kake yi.
4. Ba wanda yake so a san shi da zai yi abu a ɓoye. Da yake kana yin waɗannan abubuwa, sai ka nuna kanka ga duniya.”
5. Domin ko ʼyanʼuwansa ma ba su gaskata da shi ba.
6. Saboda haka Yesu ya ce musu, “Lokacina bai yi ba tukuna; amma a gare ku kowane lokaci daidai ne.
7. Duniya ba za ta iya ƙinku ba, amma ni take ƙi domin ina shaida cewa ayyukanta mugaye ne.
8. Ku ku tafi Bikin, ba zan in haura zuwa wannan Bikin ba yanzu, domin lokacina bai yi ba tukuna.”
9. Da ya faɗa haka, sai ya dakata a Galili.
10. Amma fa, bayan ʼyanʼuwansa suka tafi Bikin, shi ma ya tafi, ba a fili ba, amma a ɓoye.
11. A Bikin kuwa, Yahudawa suka yi ta nemansa, suna cewa, “Ina mutumin yake?”
12. A cikin taron kuwa aka yi ta raɗe-raɗe game da shi. Waɗansu suka ce, “Shi mutumin kirki ne.” Waɗansu kuwa suka ce, “Aʼa, ai, ruɗin mutane yake.”
13. Amma ba wanda ya ce kome a fili game da shi don tsoron Yahudawa.
14. Sai bayan da aka kai tsakiyar Bikin, saʼan nan Yesu ya haura zuwa filin haikali ya fara koyarwa.
15. Yahudawa suka yi mamaki suna tambaya, “Yaya wannan mutum ya sami wannan sani haka ba tare da ya yi wani karatu ba?”
16. Yesu ya amsa, ya ce, “Koyarwata ba tawa ba ce, ta fito ne daga wurin wanda ya aiko ni.
17. Duk wanda ya zaɓi yin nufin Allah, zai gane ko koyarwata daga Allah ce, ko kuwa don kaina ne nake magana.
18. Mai magana don kansa, neman ɗaukakar kansa yake yi. Amma mai neman ɗaukakar wanda ya aiko shi, shi ne mai gaskiya, ba kuwa rashin gaskiya a gare shi.
19. Ashe, ba Musa ba ne ya ba ku Doka? Duk da haka ba ko ɗayanku da yake kiyaye Dokar. Me ya sa kuke nema ku kashe ni?”
20. Taron suka amsa suka ce, “Kana da aljani, wane ne yake so yǎ kashe ka?”
21. Yesu ya ce musu, “Na yi abin banmamaki ɗaya, dukanku kuwa kuka yi mamaki.
22. Duk da haka, domin Musa ya bar muku kaciya (ko da yake a gaskiya, ba daga wurin Musa ne ya fito ba, sai dai daga wurin kakannin kakanninku), ga shi kuna yin wa yaro kaciya a ranar Asabbaci.
23. To, in za a iya yin wa yaro kaciya a ranar Asabbaci don kada a karya dokar Musa, don me kuke fushi da ni saboda na warkar da mutum a ranar Asabbaci?
24. Ku daina yin shariʼa bisa ga ganin ido, sai dai ku yi shariʼa bisa ga adalci.”
25. A nan ne fa waɗansu mutane daga Urushalima suka fara tambaya suna cewa, “Ashe, ba wannan mutum ne suke nema su kashe ba?
26. Ga shi nan yana magana a fili, su kuma ba su ce masa uffam ba. Ko hukumomi sun yarda cewa shi ne Kiristi?
27. Mun dai san inda mutumin nan ya fito; amma saʼad da Kiristi ya zo ba wanda zai san inda ya fito.”