A A A A A

Yohanna 6:52-71
52. Sai Yahudawa suka fara gardama mai tsanani a junansu suna cewa, “Yaya wannan mutum zai ba mu naman jikinsa mu ci?”
53. Sai Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, sai dai kun ci naman jikin Ɗan Mutum kuka kuma sha jininsa, ba za ku kasance da rai a cikinku ba.
54. Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana da rai madawwami. Ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.
55. Gama naman jikina abinci ne na gaskiya jinina kuma abin sha ne na gaskiya.
56. Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana cikina, ni kuma ina cikinsa.
57. Kamar dai yadda Uba mai rai ya aiko ni, ina kuma rayuwa ta saboda shi, haka ma wanda yake ni ne abincinsa zai rayu saboda ni.
58. Wannan shi ne burodin da ya sauko daga sama. Kakannin kakanninku sun ci manna suka kuma mutu, amma duk wanda yake cin wannan burodi zai rayu har abada.”
59. Ya faɗi wannan ne lokacin da yake koyarwa a cikin majamiʼa a Kafarnahum.
60. Da jin haka, da yawa daga cikin almajiransa suka ce, “Wannan koyarwa tana da wuya. Wa zai iya yarda da ita?”
61. Da yake ya san almajiransa suna gunaguni game da wannan, sai Yesu ya ce musu, “Wannan ya ɓata muku rai ne?
62. Me za ku ce ke nan, in kuka gan Ɗan Mutum yana hawa zuwa inda yake dā!
63. Ruhu ne yake ba da rai; jikin kam, ba ya amfana kome. Kalmomin da na faɗa muku, Ruhu ne, da kuma rai.
64. Duk da haka akwai waɗansunku da ba su gaskata ba.” Gama Yesu ya sani tun farko, waɗanda ba su gaskata ba, da kuma wanda zai bashe shi.
65. Ya ci gaba da cewa, “Shi ya sa na faɗa muku cewa ba mai iya zuwa wurina, sai dai Uba ya yardar masa.”
66. Daga wannan lokaci da yawa daga cikin almajiransa suka ja da baya, suka daina binsa.
67. Sai Yesu ya tambayi Sha Biyun, “Ku ma za ku tafi ne?”
68. Sai Siman Bitrus ya amsa, ya ce, “Ubangiji wajen wa za mu tafi? Kai ne da kalmomin rai madawwami.
69. Mun gaskata mun kuma san cewa kai ne Mai Tsarkin nan na Allah.”
70. Sai Yesu ya amsa, ya ce, “Ba ni na zaɓe ku Sha Biyu ba? Amma ɗayanku Iblis ne!”
71. (Yana nufin Yahuda, ɗan Siman Iskariyot, wanda, ko da yake ɗaya ne cikin Sha Biyun, zai bashe shi daga baya.)