A A A A A

Yohanna 6:22-51
22. Washegari taron da suka tsaya a wancan ƙetaren tafkin suka lura cewa jirgin ruwa ɗaya ne yake a can dā ma, kuma sun lura cewa Yesu bai shiga ciki tare da almajiransa ba, gama sun tashi su kaɗai.
23. Sai ga waɗansu jiragen ruwa daga Tibariya suka iso kusa da wurin da mutanen suka ci burodi bayan Ubangiji ya yi godiya.
24. Da taron suka lura cewa Yesu da almajiransa ba sa can, sai suka shiga jiragen ruwa suka tafi Kafarnahum neman Yesu.
25. Da suka same shi a wancan ƙetaren tafkin, sai suka tambaye shi suka ce, “Rabbi, yaushe ka kai nan?”
26. Yesu ya amsa, ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, kuna nemana ne ba don kun ga abubuwan banmamaki ba, sai dai domin kun ci burodi kun ƙoshi.
27. Kada ku yi aiki saboda abincin da yake lalacewa, sai dai saboda abinci mai dawwama har yǎ zuwa rai madawwami, wanda Ɗan Mutum zai ba ku. A kansa ne Allah Uba ya sa hatimin amincewarsa.”
28. Sai suka tambaye shi suka ce, “Me za mu yi don mu aikata ayyukan da Allah yake so?”
29. Yesu ya amsa, “Aikin Allah shi ne: a gaskata da wanda ya aiko.”
30. Sai suka tambaye shi, “Wace abin banmamaki ce za ka yi don mu gani mu kuwa gaskata ka? Me za ka yi?
31. Kakannin kakanninmu sun ci manna a hamada; kamar yadda yake a rubuce: ‘Ya ba su burodi daga sama su ci.’ ”
32. Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, ba Musa ne ya ba ku burodi daga sama ba, sai dai Ubana ne yake ba ku burodi na gaskiya daga sama.
33. Gama burodin Allah shi ne wanda yake saukowa daga sama, yana kuma ba wa duniya rai.”
34. Sai suka ce, “Ranka yǎ daɗe, daga yanzu ka dinga ba mu wannan burodi.”
35. Saʼan nan Yesu ya furta cewa, “Ni ne burodin rai. Wanda ya zo wurina ba zai taɓa jin yunwa ba, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai taɓa jin ƙishirwa ba.
36. Amma kamar yadda na faɗa muku, kun gan ni duk da haka ba ku gaskata ba.
37. Duk waɗanda Uba ya ba ni za su zo wurina, kuma duk wanda ya zo wurina ba zan kore shi ba ko kaɗan.
38. Gama na sauko daga sama ba don in cika nufin kaina ba sai dai don in cika nufin shi wanda ya aiko ni.
39. Nufin wanda ya aiko ni kuwa shi ne, kada in yi yar da ko ɗaya daga cikin duk waɗanda ya ba ni, sai dai in tashe su a rana ta ƙarshe.
40. Gama nufin Ubana shi ne, duk wanda yake duban Ɗan, ya kuma gaskata shi zai sami rai madawwami, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.”
41. Da jin haka, Yahudawa suka fara gunaguni a kansa, domin ya ce, “Ni ne burodin da ya sauka daga sama.”
42. Suka ce, “Kai, wannan ba Yesu ba ne, ɗan Yusuf, wanda mahaifinsa da mahaifiyarsa duk mun san su? Yaya yanzu zai ce, ‘Na sauko daga sama?’ ”
43. Sai Yesu ya amsa, ya ce, “Ku daina gunaguni a junanku.
44. Ba mai iya zuwa wurina, sai dai in Uban da ya aiko ni ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.
45. A rubuce yake a cikin Annabawa cewa: ‘Allah zai koyar da dukansu.’ Duk wanda ya saurari Uba, ya kuma koyi daga wurinsa, zai zo wurina.
46. Ba wanda ya taɓa ganin Uban, sai shi wanda ya zo daga Allah; shi ne kaɗai ya taɓa ganin Uban.
47. Gaskiya nake gaya muku, wanda ya gaskata yana da rai madawwami.
48. Ni ne burodin rai.
49. Kakannin kakanninku sun ci manna a hamada, duk da haka suka mutu.
50. Amma ga burodin da ya sauko daga sama, wanda mutum zai iya ci, ba zai kuma mutu ba.
51. Ni ne burodin rai mai saukowa daga sama. Duk wanda ya ci wannan burodi, shi zai rayu har abada. Wannan burodin shi ne jikina, da zan bayar don duniya ta sami rai.”