A A A A A

Luka 21:20-38
20. “In kuka ga mayaƙa sun kewaye Urushalima, za ku sani rushewarta ya yi kusa.
21. A lokacin nan, bari waɗanda suke Yahudiya, su gudu zuwa cikin duwatsu. Bari waɗanda suke cikin birnin kuma su fita, bari kuma waɗanda suke ƙauye kada su shiga birnin.
22. Gama wannan shi ne lokacin hukunci, saboda a cika duk abin da aka rubuta.
23. Zai zama abin kaito ga mata masu ciki, da mata masu renon ʼyaʼya, a waɗancan kwanakin! Za a yi baƙin ciki mai tsanani a ƙasar, da kuma fushi mai tsanani a kan mutanen nan.
24. Za a kashe su da takobi, a kuma ɗauke su ʼyan kurkuku, zuwa dukan alʼummai. Alʼummai za su tattaka Urushalima, har sai lokacin Alʼummai ya cika.
25. “Za a yi alamu a cikin rana, da cikin wata, da cikin taurari. A duniya, alʼummai za su yi baƙin ciki, su kuma rikice don tsoro, saboda ruri da kuma tafasar teku.
26. Mutane za su suma don tsoro, za su kuma yi fargaba, a kan abin da yake zuwa a bisan duniya, gama za a girgiza duniyar taurarin sararin sama.
27. A lokacin ne za su ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin girgije, da iko, da ɗaukaka mai girma.
28. Saʼad da waɗannan abubuwa sun fara faruwa, ku tashi tsaye, ku ɗaga kawunanku, domin fansarku yana matsowa kusa.”
29. Sai ya gaya musu wannan misali, ya ce, “Ku dubi itacen ɓaure da dukan itatuwa.
30. A duk lokacin da sun fara fitar da ganye, za ku gani da kanku, ku san cewa, damina ta yi kusa.
31. Haka ma, in kuka ga waɗannan abubuwa suna faruwa, ku sani mulkin Allah ya yi kusa.
32. “Gaskiya nake gaya muku, ba shakka, wannan zamani ba zai shuɗe ba, sai dukan waɗannan abubuwa sun cika.
33. Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba.
34. Ku lura fa don kada son annashuwa na banza, da shaye-shaye, da damuwa na rayuwa su rinjayi zuciyarku, har ranar ta auko muku, ba tsammani, kamar tarko.
35. Gama za ta zo a kan kowa da yake kan dukan duniya.
36. Ku yi tsaro kullum, ku yi adduʼa don ku iya kuɓuta daga dukan waɗannan abubuwa da suke kusan faruwa, don ku iya tsayawa a gaban Ɗan Mutum.”
37. Kowace rana, Yesu yakan je haikalin ya yi koyarwa, da kowace yamma kuma, ya je ya kwana a kan tudun da ake kira Dutsen Zaitun.
38. Da sassafe kuma, dukan mutanen suka zo haikalin, don su saurare shi.