English
A A A A A

Yohanna 6:1-21
1. Ɗan lokaci bayan wannan, sai Yesu ya ƙetare zuwa gaɓar mai nesa na Tekun Galili (wato, Tekun Tibariya),
2. sai taro mai yawa na mutane suka bi shi domin sun ga abubuwan banmamakin da ya yi ga marasa lafiya.
3. Saʼan nan Yesu ya hau gefen dutse ya zauna tare da almajiransa.
4. Bikin Ƙetarewan Yahudawa ya yi kusa.
5. Saʼad da Yesu ya ɗaga kai ya ga taro mai yawa suna zuwa wajensa, sai ya ce wa Filibus, “Ina za mu sayi burodi saboda mutanen nan su ci?”
6. Ya yi wannan tambayar don yǎ gwada shi ne kawai, gama ya riga ya san abin da zai yi.
7. Sai Filibus ya amsa, ya ce, “Kai, ko albashin wata takwas ba zai iya sayan isashen burodin da kowa zai ɗan samu kaɗan ba!”
8. Sai wani daga cikin almajiransa Andarawus, ɗanʼuwan Bitrus, ya yi magana,
9. “Ga wani yaro da ƙananan burodin shaʼir guda biyar da ƙananan kifi biyu, amma me wannan zai yi wa yawan mutanen nan.”
10. Yesu ya ce, “Ku sa mutanen su zauna.” Wurin kuwa akwai ciyawa da sosai, sai maza suka zazzauna, sun kai wajen dubu biyar.
11. Saʼan nan Yesu ya ɗauki burodin, ya yi godiya, ya kuma rarraba wa waɗanda suke zaune gwargwadon abin da ya ishe su. Haka kuma ya yi da kifin.
12. Saʼad da duk suka ci suka ƙoshi, sai ya ce wa almajiransa, “Ku tattara gutsattsarin da suka rage. Kada kome yǎ lalace.”
13. Saboda haka suka tattara su suka kuma cika kwanduna goma sha biyu na gutsattsarin burodin shaʼir biyar nan da suka ragu bayan kowa ya ci.
14. Bayan mutanen suka ga abin banmamakin da Yesu ya yi, sai suka fara cewa, “Lalle, wannan shi ne Annabin nan mai zuwa duniya.”
15. Da Yesu ya gane suna shirin su ɗauke shi ƙarfi da yaji su naɗa shi sarki, sai ya sāke komawa kan dutsen shi kaɗai.
16. Da yamma ta yi, sai almajiransa suka gangara zuwa tafki,
17. inda suka shiga jirgin ruwa suka tasar wa haye tafkin zuwa Kafarnahum. A lokacin kuwa duhu ya yi, Yesu kuma bai riga ya zo wurinsu ba tukuna.
18. Iska mai ƙarfi kuwa tana bugowa, ruwaye kuma suka fara hauka.
19. Bayan sun yi tuƙi wajen mil uku ko uku da rabi, sai suka ga Yesu ya kusato jirgin ruwan, yana takawa a kan ruwan; sai suka tsorata.
20. Amma ya ce musu, “Ni ne; kada ku ji tsoro.”
21. Saʼan nan suka yarda suka karɓe shi a cikin jirgin ruwan, nan da nan kuwa jirgin ya kai gaɓar da za su.