English
A A A A A

Yohanna 5:1-23
1. Bayan an ɗan jima, sai Yesu ya haura zuwa Urushalima don wani bikin Yahudawa.
2. To, a Urushalima akwai wani tafki kusa da Ƙofar Tumaki, wanda a yaren Aramayik ake kira Betesda da Aramayik, an kuma kewaye shi da shirayi biyar.
3. A nan naƙasassu da yawa sukan kwanta-makafi, guragu, shanyayyu.
4. ***
5. Akwai wani da yake nan ba shi da amfani shekara talatin da takwas.
6. Da Yesu ya gan shi kwance a can ya kuma sami labari cewa ya daɗe a wannan hali, sai ya tambaye shi, “Kana so ka warke?”
7. Marar amfanin nan ya ce, “Ranka yǎ daɗe, ba ni da wanda zai taimaka yǎ sa ni a cikin tafkin saʼad da aka motsa ruwan. Yayinda nake ƙoƙarin shiga, sai wani yǎ riga ni.”
8. Sai Yesu ya ce masa, “Tashi! Ɗauki tabarmarka ka yi tafiya.”
9. Nan take mutumin ya warke; ya ɗauki tabarmarsa ya yi tafiya. A ranar da wannan ya faru ranar Asabbaci ce,
10. saboda haka kuwa Yahudawa suka ce wa mutumin da aka warkar, “Yau Asabbaci ne; doka ta hana ka ɗauki tabarmarka.”
11. Amma ya amsa, ya ce, “Mutumin da ya warkar da ni shi ya ce mini, ‘Ɗauki tabarmarka ka yi tafiya.’ ”
12. Sai suka tambaye shi suka ce, “Wane ne wannan da ya ce maka ka ɗauke ta ka yi tafiya?”
13. Mutumin da aka warkar kuwa bai ma san ko wane ne ba ne, gama Yesu ya ɓace cikin taron da yake can.
14. Daga baya Yesu ya same shi a haikali ya ce masa, “Ga shi, ka warke. Ka daina yin zunubi, in da haka ba wani abin da ya fi wannan muni zai iya samunka.”
15. Sai mutumin ya je ya gaya wa Yahudawa cewa Yesu ne ya warkar da shi.
16. To, domin Yesu yana yin waɗannan abubuwa a ranar Asabbaci, sai Yahudawa suka tsananta masa.
17. Yesu ya ce musu, “Ubana yana cikin aikinsa kullum har yǎ zuwa wannan rana, haka ni ma, ina kan aiki.”
18. Don haka Yahudawa suka ƙara nema su kashe shi; ba don ya karya Asabbaci kawai ba, har ma yana ce Allah Ubansa ne, yana mai da kansa daidai da Allah.
19. Sai Yesu ya ba su wannan amsa cewa, “Gaskiya nake gaya muku, Ɗan ba ya iya yin kome da kansa; yana yin abin da ya ga Ubansa yake yi ne kawai, gama duk abin da Uban yake yi shi ne Ɗan ma yake yi.
20. Gama Uban yana ƙaunar Ɗan yana kuma nuna masa duk abin da yake yi. I, za ku kuwa yi mamaki, gama zai nuna masa abubuwan da suka fi waɗannan girma.
21. Gama kamar yadda Uban yake ta da matattu yake kuma ba su rai, haka ma Ɗan yake ba da rai ga wanda ya ga dama.
22. Bugu da ƙari, Uban ba ya hukunta kowa, sai dai ya danƙa dukan hukunci a hannun Ɗan,
23. don kowa yǎ girmama Ɗan kamar yadda yake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan ba ya girmama Uban, da ya aiko shi ke nan.