A A A A A

Yohanna 4:1-30
1. Sai Farisiyawa suka ji cewa Yesu yana samun yana kuma yi wa almajirai da yawa baftisma fiye da Yohanna,
2. ko da yake ba Yesu ne yake baftismar ba, sai almajiransa.
3. Da Ubangiji ya sami wannan labari, sai ya bar Yahudiya ya sāke koma Galili.
4. To, ya zama dole yǎ bi ta Samariya.
5. Sai ya zo wani gari a Samariya da ake ce da shi Saikar, kurkusa da filin da Yaƙub ya ba wa ɗansa Yusuf.
6. Rijiyar Yaƙub kuwa tana can, Yesu kuwa, saboda gajiyar tafiya, sai ya zauna a bakin rijiyar. Wajen saʼa ta shida ne.
7. Saʼad da wata Basamariya ta zo ɗiban ruwa, sai Yesu ya ce mata, “Za ki ba ni ruwa in sha?”
8. (Almajiransa kuwa sun shiga gari don sayi abinci.)
9. Sai Basamariyar ta ce masa, “Kai Bayahude ne ni kuwa Basamariya ce. Yaya za ka roƙe ni ruwan sha?” (Don Yahudawa ba sa hulɗa da Samariyawa).
10. Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah da kuma wanda yake roƙonki ruwan sha, da kin roƙe shi, da shi kuwa ya ba ki ruwan rai.”
11. Sai macen ta ce, “Ranka yǎ daɗe, ba ka da guga rijiyar kuwa tana da zurfi. Ina za ka sami wannan ruwan rai?
12. Ka fi mahaifinmu Yaƙub ne, wanda ya ba mu rijiyar ya kuma sha daga ciki da kansa, haka ma ʼyaʼyansa da kuma garkunan shanunsa da tumakinsa?”
13. Yesu ya amsa, ya ce, “Kowa da ya sha wannan ruwa zai sāke jin ƙishirwa,
14. amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi ba zai ƙara jin ƙishirwa ba. Lalle, ruwan da zan ba shi zai zama maɓuɓɓugan ruwa a cikinsa da yake ɓuɓɓugowa har yǎ zuwa rai madawwami.”
15. Sai macen ta ce masa, “Ranka yǎ daɗe, ka ba ni ruwan nan don kada in ƙara jin ƙishirwa in yi ta zuwa nan ɗiban ruwa.”
16. Sai ya ce mata, “Je ki kira mijinki ki dawo.”
17. Ta ce, “Ai, ba ni da miji.” Sai Yesu ya ce mata, “Gaskiyarki da kika ce ba ki da miji.
18. Gaskiyar ita ce, kin auri maza biyar, mutumin da kike da shi yanzu ba mijinki ba ne. Abin da kika faɗa yanzu gaskiya ne.”
19. Sai macen ta ce, “Ranka yǎ daɗe, na gane kai annabi ne.
20. Kakanninmu sun yi sujada a kan dutsen nan, amma ku Yahudawa ɗauka cewa inda ya kamata mu yi sujada shi ne Urushalima.”
21. Sai Yesu ya ce, “Ina tabbatar miki, mace, lokaci yana zuwa da ba za ku yi wa Uba sujada ko a kan dutsen nan ko kuma a Urushalima ba.
22. Ku Samariyawa kuna yi wa abin da ba ku sani ba sujada; mu kuwa muna yi wa abin da muka sani ne sujada, gama ceto daga Yahudawa yake.
23. Duk da haka lokaci yana zuwa har ma ya riga ya yi da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada cikin Ruhu da kuma gaskiya, domin irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema.
24. Allah ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa dole su yi masa sujada cikin ruhu da kuma cikin gaskiya.”
25. Macen ta ce, “Na san cewa Almasihu, (da ake ce da shi Kiristi) yana zuwa. Saʼad da ya zo kuwa, zai bayyana mana kome.”
26. Sai Yesu ya ce, “Ai, ni ɗin nan da yake magana da ke, Ni ne shi.”
27. Nan take sai almajiransa suka dawo suka kuma yi mamakin ganinsa yana magana da mace. Amma ba wanda ya ce, “Me kake so?” Ko “Me ya sa kake magana da ita?”
28. Sai macen ta bar tulunta na ruwa, ta koma cikin gari ta ce wa mutane,
29. “Ku zo, ku ga mutumin da ya gaya mini duk abin da na taɓa yi. Shin, ko shi ne Kiristi?”
30. Sai suka fito daga garin suka nufo inda yake.