English
A A A A A

Yohanna 3:1-18
1. Akwai wani Bafarisiye mai suna Nikodimus, wani ɗan majalisar Yahudawa.
2. Ya zo wurin Yesu da dad dare ya ce, “Rabbi, mun sani kai malami ne daga Allah. Gama ba wanda zai iya yin waɗannan abubuwan banmamaki da kake yi in Allah ba ya tare da shi.”
3. Yesu ya amsa, ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an sāke haihuwarsa.”
4. Nikodimus ya yi tambaya, ya ce, “Yaya za a haifi mutum saʼad da ya tsufa? Hakika ba zai sāke koma sau na biyu cikin cikin mahaifiyarsa don a haife shi ba!”
5. Yesu ya amsa, ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an haife shi ta wurin ruwa da kuma Ruhu.
6. Jiki yakan haifi jiki, amma Ruhu yana haifi ruhu.
7. Kada ka yi mamaki da na ce, ‘Dole ne a sāke haifarku.’
8. Iska takan hura zuwa inda take so. Kai kakan ji motsinta, sai dai ba ka iya sanin inda take fitowa ko kuwa inda za ta. Haka yake ga duk wanda aka haifa ta wurin Ruhu.”
9. Nikodimus ya yi tambaya, ya ce, “Yaya wannan zai yiwu?”
10. Yesu ya ce, “Kai ma da kake malami na Israʼila, ba ka fahimci waɗannan abubuwa ba?
11. Gaskiya nake faɗa maka, muna magana a kan abin da muka sani, muka kuma shaida abin da muka gani ne, amma har yanzu kun ƙi ku karɓi shaidarmu.
12. Na yi muku magana a kan abubuwan duniya amma ba ku gaskata ba; to, yaya za ku gaskata in na yi magana a kan abubuwan sama?
13. Ba wanda ya taɓa hawa zuwa sama sai wanda ya sauka daga sama-Ɗan Mutum.
14. Kamar dai yadda Musa ya ɗaga maciji a hamada, haka dole ne a ɗaga Ɗan Mutum,
15. don duk mai gaskata da shi ya sami rai madawwami.
16. “Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yǎ hallaka sai dai yǎ sami rai madawwami.
17. Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yǎ yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yǎ ceci duniya ta wurinsa.
18. Duk wanda ya gaskata da shi ba za a yi masa hukunci ba, amma duk wanda bai gaskata ba an riga an yi masa hukunci domin bai gaskata da sunan wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗan Allah ba.