A A A A A

Yohanna 1:29-51
29. Washegari Yohanna ya ga Yesu yana zuwa wajensa sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah mai ɗauke zunubin duniya!
30. Wannan shi ne wanda nake nufi saʼad da na ce, ‘Wani mai zuwa bayana ya fi ni girma, domin yana nan kafin ni.’
31. Ko ni ma dā ban san shi ba, sai dai abin da ya sa na zo ina baftisma da ruwa shi ne domin a bayyana shi ga Israʼila.”
32. Sai Yohanna ya ba da wannan shaida: “Na ga Ruhu ya sauko kamar kurciya daga sama ya zauna a kansa.
33. Dā ban san shi ba, sai dai wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa ya gaya mini cewa, ‘Mutumin da ka ga Ruhu ya sauko ya kuma zauna a kansa shi ne wanda zai yi baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’
34. Na gani na kuma shaida cewa wannan Ɗan Allah ne.”
35. Washegari kuma Yohanna yana can tare da biyu daga cikin almajiransa.
36. Da ya ga Yesu yana wucewa, sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah!”
37. Da almajiran nan biyu suka ji ya faɗi haka, sai suka bi Yesu.
38. Da juyewa, sai Yesu ya ga suna binsa, sai ya tambaye, su ya ce, “Me kuke nema?” Suka ce, “Rabbi,” (wato, Malam), “ina kake da zama?”
39. Ya amsa musu ya ce, “Ku zo, za ku kuma gani.” Saboda haka suka je suka ga inda yake da zama, suka kuma zauna a can tare da shi. Wajen saʼa ta goma ce kuwa.
40. Andarawus ɗanʼuwan Siman Bitrus, yana ɗaya daga cikin biyun da suka ji abin da Yohanna ya faɗa wanda kuma ya bi Yesu.
41. Abu na fari da Andarawus ya yi shi ne ya sami ɗanʼuwansa Siman ya gaya masa cewa, “Mun sami Almasihu” (wato, Kiristi).
42. Ya kuma kawo shi wurin Yesu. Yesu ya dube shi ya ce, “Kai ne Siman ɗan Yohanna. Za a ce da kai Kefas” (in an fassara, Bitrus ke nan  ).
43. Washegari Yesu ya yanke shawara yǎ tafi Galili. Da ya sami Filibus sai ya ce masa, “Bi ni.”
44. Filibus, kamar Andarawus da Bitrus shi ma daga garin Betsaida ne.
45. Filibus ya sami Natanayel ya kuma gaya masa, “Mun sami wanda Musa ya rubuta game da shi a cikin Doka, kuma wanda annabawa suka rubuta a kansa-Yesu Banazare, ɗan Yusuf.”
46. Natanayel ya ce, “A Nazaret! Wani abin kirki zai iya fito daga can?” Filibus ya ce, “Zo ka gani.”
47. Da Yesu ya ga Natanayel yana zuwa, sai ya yi magana game da shi cewa, “Ga mutumin Israʼila na gaske wanda ba shi da haʼinci.”
48. Natanayel ya yi tambaya, ya ce, “A ina ka san ni?” Yesu ya amsa, ya ce, “Na gan ka yayinda kake a gindin itacen ɓaure, kafin Filibus yǎ kira ka.”
49. Sai Natanayel ya ce, “Rabbi, kai Ɗan Allah ne. Kai ne Sarkin Israʼila.”
50. Yesu ya ce, “Ka gaskata domin na ce maka na gan ka a gindin itacen ɓaure. Za ka ga abubuwan da suka fi haka.”
51. Sai ya ƙara da cewa, “Gaskiya nake gaya muku, za ku ga sama a buɗe, malaʼikun Allah kuma suna hawa suna kuma sauka a kan Ɗan Mutum.”