A A A A A

Yohanna 1:1-28
1. Tun fara farawa akwai Kalma, Kalman kuwa yana nan tare da Allah, Kalman kuwa Allah ne.
2. Yana nan tare da Allah tun fara farawa.
3. Ta wurinsa ne aka halicci dukan abubuwa; in ba tare da shi ba, babu abin da aka yi wanda aka yi.
4. A cikinsa rai ya kasance, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane.
5. Hasken yana haskakawa cikin duhu, amma duhun bai rinjaye shi ba.
6. Akwai wani mutumin da aka aiko daga Allah; mai suna Yohanna.
7. Ya zo a matsayin mai shaida domin yǎ ba da shaida game da wannan haske, don ta wurinsa dukan mutane su ba da gaskiya.
8. Shi kansa ba shi ne hasken ba; sai dai ya zo a matsayin shaida ne kaɗai ga hasken.
9. Haske na gaskiya da yake ba da haske ga kowane mutum mai shigowa duniya.
10. Yana a duniya, kuma ko da yake an yi duniya ta wurinsa ne, duniya ba ta gane shi ba.
11. Ya zo wurin abin da yake nasa, amma nasa ɗin ba su karɓe shi ba.
12. Duk da haka dukan waɗanda suka karɓe shi, ga waɗanda suka gaskata a sunansa, ya ba su iko su zama ʼyaʼyan Allah— 
13. ʼyaʼyan da aka haifa ba bisa hanyar ʼyan adam, ko shawarar mutum ko nufin namiji ba, sai dai haifaffu bisa ga nufin Allah.
14. Kalman ya zama mutum, ya kuwa zauna a cikinmu. Muka ga ɗaukakarsa, ɗaukaka ta wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaici, wanda ya zo daga wurin Uba, cike da alheri da gaskiya.
15. Yohanna ya ba da shaida game da shi. Ya ɗaga murya yana cewa, “Wannan shi ne wanda na ce, ‘Mai zuwa bayana ya fi ni girma domin yana nan kafin ni.’ ”
16. Daga yalwar alherinsa dukanmu muka sami albarka bisa albarka.
17. Gama an ba da doka ta wurin Musa; alheri da gaskiya kuwa sun zo ne ta wurin Yesu Kiristi.
18. Ba wanda ya taɓa ganin Allah, sai dai Allah da yake Ɗaya da kuma Makaɗaici wanda yake a gefen Uba, shi ne ya bayyana shi.
19. To, ga shaidar Yohanna saʼad da Yahudawan Urushalima suka aiki firistoci da Lawiyawa su tambaye shi ko shi wane ne.
20. Bai yi mūsu ba, amma ya shaida a fili cewa, “Ba ni ne Kiristi ba.”
21. Sai suka tambaye shi suka ce, “To, wane ne kai? Kai ne Eliya?” Ya ce, “Aʼa, ni ba shi ba ne.” “Kai ne Annabin nan?” Ya amsa ya ce, “Aʼa.”
22. A ƙarshe suka ce, “Wane ne kai? Ka ba mu amsa don mu mayar wa waɗanda suka aike mu. Me kake ce da kanka?”
23. Yohanna ya amsa da kalmomin annabi Ishaya, “Ni murya ne mai kira a hamada, ‘Ku miƙe hanya domin Ubangiji.’ ”
24. To, waɗansu Farisiyawan da aka aika
25. suka tambaye shi suka ce, “Don me kake yin baftisma in kai ba Kiristi ba ne, ba kuwa Eliya ba, ba kuma annabin nan ba?”
26. Yohanna ya amsa, ya ce, “Ni dai ina baftisma da ruwa ne, amma a cikinku akwai wani tsaye da ba ku sani ba.
27. Shi ne mai zuwa bayana, wanda ko igiyar takalmansa ma ban isa in kunce ba.”
28. Wannan duk ya faru ne a Betani a ƙetaren Urdun, inda Yohanna yake yin baftisma.