A A A A A

Luka 21:1-19
1. Da Yesu ya ɗaga ido, sai ya ga waɗansu masu arziki suna sa baikonsu a maʼajiyin haikalin.
2. Ya kuma ga wata gwauruwa matalauciya, ta saka anini biyu.
3. Sai ya ce, “Gaskiya ina faɗa muku, wacce nan gwauruwa matalauciya ta sa fiye da dukan sauran.
4. Dukan mutanen nan sun ba da baikonsu daga cikin arzikinsu ne, amma ita daga cikin talaucinta, ta saka duk abin da take da shi na rayuwa.”
5. Waɗansu daga cikin almajiransa, suka fara magana a kan yadda aka yi wa haikalin ado da duwatsu masu kyau, da kuma kyautai da aka keɓe wa Allah. Amma Yesu ya ce,
6. “Wannan abin da kuke ƙallo a nan, lokaci yana zuwa da ba za a bar wani dutse a kan wani dutse ba. Kowanensu, za a rushe shi.”
7. Suka tambaye shi suka ce, “Malam, yaushe waɗannan za su faru? Kuma wace alama za ta nuna cewa suna dab da faruwa?”
8. Ya amsa ya ce, “Ku lura, kada ku kuma a ruɗe ku. Gama da yawa za su zo a cikin sunana, suna cewa, ‘Ai, ni ne shi,’ da kuma, ‘Lokaci ya yi kusa.’ Kada ku bi su.
9. Saʼad da kuka ji labarin yaƙe-yaƙe, da juye juyen mulki, kada ku tsorota. Dole ne waɗannan abubuwa su fara faruwa, amma ƙarshen ba zai zo nan da nan ba.”
10. Sai ya ce musu, “Alʼumma za ta tasar wa alʼumma, mulki zai tasar wa mulki.
11. Za a yi manyan girgizan ƙasa, da yunwa, da annoba a wurare dabam-dabam, da kuma abubuwa masu bantsoro, da manyan alamu daga sama.
12. “Amma kafin duk abubuwa nan, za a kama ku a tsananta muku. Za a kai ku majamiʼu, da kurkuku. Za a kuma kai ku gaban sarakuna da gwamnoni, kuma dukan waɗannan saboda sunana.
13. Wannan zai sa ku zama shaidu a gare su.
14. Amma ku yi ƙuduri, wato, ku shirya zuciyarku, a kan ba za ku damu ba kafin lokacin, game da yadda da za ku kāre kanku.
15. Gama zan ba ku kalmomi, da hikima waɗanda ba ko ɗaya daga cikin maƙiyanku, za su iya tsayayya da ku, ko su ƙaryata.
16. Har iyayenku, da ʼyanʼuwanku maza, da danginku, da abokanku ma, duk za su bashe ku, su kuma kashe waɗansunku.
17. Duk mutane za su ƙi ku saboda ni.
18. Amma ko gashi ɗaya na kanku, ba zai hallaka ba.
19. Ta wurin tsayawa da ƙarfi, za ku sami rai.