English
A A A A A

Luka 9:37-62
37. Washegari, saʼad da Yesu tare da almajiran nan uku suka sauka daga kan dutsen, sai taro mai yawa ya haɗu da shi.
38. Sai wani mutum daga cikin taron ya yi kira da ƙarfi, ya ce, “Malam, ina roƙonka, ka dubi ɗan nan nawa, gama shi ne kaɗai nake da shi.
39. Wani ruhu yakan kama shi, sai ya yi ihu farar ɗaya. Yakan sa shi farfaɗiya, har bakinsa ya yi kumfa. Da ƙyar yake barinsa, yana kuwa kan hallakar da shi.
40. Na roƙi almajiranka su fitar da shi, amma ba su iya ba.”
41. Yesu ya amsa, ya ce, “Ya karkataccen zamani marar bangaskiya, har yaushe ne zan kasance tare da ku, ina kuma haƙuri da ku? Kawo yaronka nan.”
42. Yaron yana kan zuwa ke nan, sai aljanin ya buga shi ƙasa, cikin farfaɗiya. Amma Yesu ya kwaɓe mugun ruhun, ya warkar da yaron, sai ya miƙa shi ga mahaifinsa.
43. Duk suka yi mamakin girman Allah. Yayinda kowa yana cikin mamakin dukan abubuwan da Yesu ya yi, sai ya ce wa almajiransa,
44. “Ku kasa kunne da kyau ga abin da zan faɗa muku. Za a bashe Ɗan Mutum ga hannun mutane.”
45. Amma ba su fahimci abin da yake nufi da wannan magana ba. Ba su gane ba, don an ɓoye musu shi. Su kuwa sun ji tsoro su tambaye shi.
46. Wata gardama ta tashi a tsakanin almajiran, a kan ko wane ne a cikinsu zai zama mafi girma
47. Da yake Yesu ya san tunaninsu, sai ya ɗauki wani ƙaramin yaro, ya sa ya tsaya kusa da shi.
48. Sai ya ce musu, “Duk wanda ya karɓi wannan ƙaramin yaron a cikin sunana, ni ya karɓa, kuma duk wanda ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne. Gama mafi ƙanƙanta duka a cikinku, shi ne kuma mafi girma.”
49. Sai Yohanna, ya ce, “Ubangiji, mun ga wani mutum yana fitar da aljanu a cikin sunanka, muka yi ƙoƙarin hana shi, don shi ba ɗaya ba ne daga cikinmu.”
50. Yesu ya ce, “Kada ku hana shi, gama duk wanda ba ya gāba da ku, naku ne.”
51. Da lokaci ya yi kusa da za a ɗauki Yesu zuwa sama, sai ya ɗaura niyyar tafiya Urushalima.
52. Sai ya aiki ʼyan saƙo, su yi gaba. Su kuwa, suka shiga cikin wani ƙauyen Samariyawa, don su shirya masa abubuwa.
53. Amma mutanen ƙauyen ba su karɓe shi ba, don yana kan hanyar zuwa Urushalima ne.
54. Da almajiransa, Yaƙub da Yohanna suka ga haka, sai suka tambaya, “Ubangiji, kana so mu kira wuta ta sauka daga sama ta hallaka su?”
55. Amma Yesu ya juya, ya kwaɓe su.
56. Sai suka tafi wani ƙauye.
57. Suna kan tafiya a hanya, sai wani mutum ya ce masa, “Zan bi ka, duk inda za ka.”
58. Yesu ya amsa, ya ce, “Yanyawa suna da ramummuka, tsuntsayen sararin sama kuma suna da sheƙa, wato, wurin kwanansu, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin da zai sa kansa ba.”
59. Ya kuma ce wa wani mutum, “Ka bi ni.” Amma mutumin ya amsa, ya ce, “Ubangiji, bari in je in binne mahaifina tukuna.”
60. Yesu ya ce masa, “Ka bar matattu su binne matattunsu, amma kai, ka je ka yi shelar mulkin Allah.”
61. Har wa yau, wani ya ce, “Zan bi ka, Ubangiji, amma ka bar ni in je in yi bankwana da iyalina tukuna.”
62. Yesu ya amsa, ya ce, “Babu wani da yakan sa hannunsa a garman shanu, saʼan nan ya waiwaya baya, da ya isa ya shiga hidima a cikin mulkin Allah ba.”