A A A A A

Luka 9:18-36
18. Wata rana saʼad da Yesu yana adduʼa a ɓoye, almajiransa kuma suna tare da shi, sai ya tambaye, su ya ce, “Wa, taron mutane ke ce da ni?”
19. Suka amsa, suka ce, “Waɗansu suna cewa, Yohanna Mai Baftisma, waɗansu kuma annabi Eliya, har wa yau waɗansu suna cewa, kai ɗaya daga cikin annabawan da ne, da ya tashi da rai.”
20. “Amma ku fa, wa, kuke ce da ni?” Bitrus ya amsa, ya ce, “Kiristi na Allah.”
21. Yesu ya gargaɗe su da ƙarfi, kada su gaya wa kowa wannan magana.
22. Ya sāke cewa, “Dole ne Ɗan mutum ya sha wahaloli da yawa, dattawa, da manyan firistoci, da malaman dokoki kuma su ƙi shi, kuma dole a kashe shi, a rana ta uku kuma a ta da shi da rai.”
23. Sai ya ce wa dukansu, “In wani zai bi ni, dole ya musanta kansa, ya ɗauki gicciyensa kowace rana, ya bi ni.
24. Gama duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni zai same shi.
25. Ina amfani, in mutum ya ribato duniya duka, amma ya rasa ransa, ko kuma ya yi hasarar ransa.
26. Duk wanda yake jin kunyana da na kalmomina, Ɗan Mutum ma zai ji kunyarsa saʼad da zai zo a cikin ɗaukakarsa, da ɗaukakar Uban, da kuma ta tsarkaka malaʼikun.
27. Gaskiya nake gaya muku, waɗansu da suke tsattsaye a nan ba za su ga mutuwa ba, sai sun ga mulkin Allah.”
28. Bayan kamar kwana takwas da yin wannan magana, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yohanna, da kuma Yaƙub, suka hau kan dutse tare don yin adduʼa.
29. Yana cikin adduʼa, sai kamannin fuskarsa ta sāke, tufafinsa kuma suka zama da haske kamar hasken walƙiya.
30. Sai ga mutum biyu, Musa da Eliya,
31. suka bayyana cikin kyakkyawar daraja, suna magana da Yesu. Suka yi zance a kan tashinsa, wanda shi ya kusan ya kawo ga cikarsa a Urushalima.
32. Barci kuwa ya kama Bitrus da abokan tafiyarsa sosai. Da idanunsu suka warware, sai suka ga ɗaukakarsa da kuma mutum biyun tsaye tare da shi.
33. Da mutanen na barin Yesu, sai Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, ya yi kyau da muke nan. Bari mu kafa bukkoki guda uku, wato, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Eliya.” (Bai ma san abin da yake faɗi ba.)
34. Yayinda yake cikin magana, sai wani girgije ya bayyana ya rufe su, sai suka ji tsoro, yayinda suke shiga cikin girgijen.
35. Wata murya ta fito daga cikin girgijen, tana cewa, “Wannan Ɗana ne, zaɓaɓɓena, ku saurare shi.”
36. Da muryar ta gama magana, sai suka tarar Yesu shi kaɗai ne. Almajiran kuwa suka riƙe wannan alʼamari a zukatansu. A lokacin nan, ba su gaya wa kowa abin da suka gani ba.