A A A A A

Luka 8:26-56
26. Suka shiga jirgin ruwa zuwa yankin Gerasenawa da yake a hayin tafkin, daga wajen Galili.
27. Da Yesu ya sauka daga jirgin, sai ga wani mutum mai aljanu daga garin: Mutumin ya daɗe bai sa tufafi ba, kuma ba ya zama a gida. Yana zama a cikin kaburbura.
28. Da ya ga Yesu, sai mutumin ya ɗaga murya da ƙarfi, ya fāɗi a gabansa, yana ihu cewa, “Ina ruwanka da ni, Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ina roƙonka, kada ka ba ni wahala!”
29. Gama Yesu ya riga ya umarci mugun ruhun ya fita daga mutumin. Sau da yawa mugun ruhun yakan sha kamunsa. Ko da yake akan ɗaure shi hannu da ƙafa, da sarƙa, a kuma yi gadinsa, amma yakan tsinke sarƙoƙinsa, aljanun kuma su kore shi zuwa wuraren kaɗaici, inda ba kowa.
30. Yesu ya tambaye shi, “Mene ne sunanka?” Sai ya amsa, “Legiyon,” wato, “Tuli,” gama aljanu masu ɗumbun yawa ne suna cikinsa.
31. Suka yi ta roƙonsa kada ya umarce su su shiga ramin Abis.
32. A wurin kuwa, akwai babban garken aladu da suke kiwo a gefen tudu. Aljanun suka roƙi Yesu ya bar su, su shiga cikin aladun, ya kuwa yardar musu.
33. Da aljanun suka fita daga cikin mutumin, sai suka shiga cikin aladun. Garken kuma ya gangara daga kan tudun zuwa cikin tafkin, kuma suka nutse.
34. Da masu kiwon aladun suka ga abin da ya faru, sai suka ruga da gudu zuwa garin da yakewaye suka kai labari.
35. Mutanen kuma suka fito don su ga abin da ya faru. Da suka iso wurin Yesu, sai suka tarar da mutumin da aljanun suka fita daga cikinsa, yana zaune kusa da Yesu sanye da tufafi, kuma cikin hankalinsa, sai tsoro ya kama su.
36. Waɗanda suka ga abin da faru, suka gaya wa mutanen yadda aka warkar da mai aljanun.
37. Sai dukan mutanen yankin Gerasenawa suka roƙi Yesu ya bar su, don sun tsorata sosai. Sai Yesu ya shiga jirgin ruwa ya tafi.
38. Mutumin da aka fitar da aljanun daga cikinsa, ya roƙi Yesu don ya tafi tare da shi, amma Yesu ya sallame shi, ya ce,
39. “Koma gida, ka shaida babban alherin da Allah ya yi maka.” Sai mutumin ya tafi yana faɗin abin da Yesu ya yi masa a duk garin.
40. Da Yesu ya koma, taron suka marabce shi, don dā ma duk suna jiransa.
41. Sai wani mutum mai suna Yayirus, wani mai mulkin majamiʼa, ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, yana roƙonsa ya zo gidansa,
42. domin diyarsa ɗaya tak, wadda ta kai shekara goma sha biyu, tana bakin mutuwa. Da Yesu yake kan hanyarsa, taron mutane masu yawa suka yi ta matsa shi a kowane gefe.
43. A wurin kuwa, akwai wata mace wadda tana da ciwon zubar da jini, har na shekara goma sha biyu, amma babu wanda ya iya warkar da ita.
44. Sai ta zo ta bayansa, ta taɓa bakin rigarsa. Nan da nan, zubar da jininta ya tsaya.
45. Yesu ya yi tambaya, “Wa ya taɓa ni?” Bayan kowa ya yi musu, sai Bitrus ya ce, “Ubangiji, ai, mutane da yawa suna matsinka ta kowane gefe.”
46. Amma Yesu ya ce, “Wani ya taɓa ni, na san cewa iko ya fita daga wurina.”
47. Sai macen, da ta ga ba halin ɓoyewa, sai ta fita, jikinta na rawa, ta fāɗi a gabansa. A gaban dukan mutanen, ta faɗi dalilin da ya sa ta taɓa shi, da yadda ta warke nan take.
48. Sai Yesu ya ce mata, “Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki tafi cikin salama.”
49. Yayinda Yesu na cikin magana har yanzu, sai ga wani daga gidan Yayirus, mai mulkin majamiʼar, ya ce, “Kada ka ƙara damun malam, diyarka ta rasu.”
50. Da Yesu ya ji wannan, sai ya ce wa Yayirus, “Kada ka ji tsoro, ka gaskata, za a kuma warkar da ita.”
51. Da ya iso gidan Yayirus, sai ya hana kowa ya bi shi cikin ɗakin, sai dai Bitrus, da Yohanna, da Yaƙub, da kuma mahaifin da mahaifiyar.
52. Ana cikin haka, dukan mutanen kuma sai kuka da makoki suke ta yi, domin yarinyar. Sai Yesu ya ce, “Ka daina yin kuka, ba ta mutu ba, tana barci ne.”
53. Sai suka yi masa dariya, da yake sun san cewa, ta mutu.
54. Amma Yesu ya kama ta a hannu ya ce, “Diyata, ki tashi.”
55. Ruhunta ya dawo, kuma ta tashi, nan take. Yesu ya ce musu, su ba ta wani abu ta ci.
56. Iyayenta suka yi mamaki, amma ya ba su umarni kada su faɗa wa kowa abin da ya faru.