A A A A A

Luka 8:1-25
1. Bayan wannan sai Yesu ya zazzaga gari da ƙauye, yana waʼazin bisharar mulkin Allah. Sha Biyun nan kuwa suna tare da shi,
2. da kuma waɗansu mata waɗanda aka warkar da su daga cututtukansu, da kuma mugayen ruhohi. Cikinsu akwai Maryamu, (wadda ake kira Magdalin) wadda aljanu bakwai suka fito daga cikinta.
3. Da Yowanna matar Kuza, manajan iyalin Hiridus; da Suzana; da waɗansu mata da yawa. Waɗannan mata suna taimaka musu cikin hidima, daga cikin abin da suke da shi na zaman gari.
4. Yayinda taron mai girma na taruwa, mutane kuma daga garuruwa dabam-dabam suna zuwa wurin Yesu, sai ya ba da wannan misali, ya ce,
5. “Wani manomi ya fita domin ya shuka irinsa. Da yana watsa irin, sai waɗansu suka fāɗi a kan hanya, aka tattaka su, tsuntsayen sararin sama kuma suka cinye su.
6. Waɗansu suka fāɗi a kan dutse, da suka tsira sai suka yanƙwane don rashin danshi.
7. Waɗansu kuma suka fāɗi a cikin ƙaya. Da suka yi girma tare, sai ƙayan suka shaƙe su.
8. Waɗansu kuma har yanzu, suka fāɗi a ƙasa mai kyau, suka yi girma, suka ba da amfani riɓi ɗari ɗari, fiye da abin da aka shuka.” Da faɗin haka sai ya ce, “Duk mai kunnen ji, yǎ ji.”
9. Almajiransa suka tambaye shi maʼanar wannan misali.
10. Sai ya ce, “Ku ne aka ba sanin asirin mulkin Allah, amma ga sauran mutane kam, ina magana da misalai, saboda, “ ‘ko da yake suna ƙallo, ba za su gani ba, ko da yake suna ji, ba za su gane ba.’ 
11. “Ga maʼanar misalin: irin, shi ne maganar Allah.
12. Waɗanda suka fāɗi a kan hanya su ne mutanen da suka ji, amma Iblis, yakan zo ya ɗauke maganar daga zuciyarsu, don kada su gaskata, su sami ceto.
13. Na kan dutse kuwa, su ne da jin maganar, sukan karɓa da murna, amma ba su da saiwa. Sukan gaskata na ɗan lokaci, amma lokacin gwaji, sai su ja da baya.
14. Irin da suka fāɗi a cikin ƙaya kuwa, su ne mutanen da suka ji, amma a kwana a tashi, tunanin kayan duniya, da neman arziki, da son jin daɗi, sukan hana su ba da ʼyaʼya.
15. Amma irin da suka fāɗi a ƙasa mai kyau kuwa, su ne mutane masu kyakkyawar zuciya, mai kyau, da suka ji, suka riƙe, suka kuma jimre har suka ba da ʼyaʼya.”
16. “Ba mai ƙuna fitila saʼan nan ya ɓoye ta a cikin tulu, ko kuma ya sa ta a ƙarƙashin gado ba. A maimakon haka, yakan sa ta a kan alkuki, saboda mutane masu shigowa su ga haske.
17. Ba abin da yake ɓoye da ba za a fallasa ba. Kuma ba abin da yake rufe, da ba za a sani ba, ko a fitar da shi a fili ba.
18. Saboda haka, ku yi tunani da kyau yadda kuke saurara. Duk wanda yake da shi, za a ƙara masa, duk wanda ba shi da shi kuma, abin da yake tsammani yana da shi ma, za a karɓe daga gare shi.”
19. Sai uwar Yesu da ʼyanʼuwansa suka zo, domin su gan shi, amma ba su iya zuwa kusa da shi ba, saboda taron.
20. Sai wani ya faɗa masa cewa, “Ga uwarka da ʼyanʼuwanka suna tsaye a waje suna so su gan ka.”
21. Ya amsa ya ce, “Uwana da ʼyanʼuwana, su ne waɗanda suke jin maganar Allah, suna kuma aikata ta.”
22. Wata rana Yesu ya ce wa almajiransa, “Mu haye zuwa wancan gefen tafkin.” Sai suka shiga jirgin ruwa suka fara tafiya.
23. Da suna cikin tafiya, sai barci ya kwashe shi. Sai wata babban iska ta taso kan tafkin, har ruwa ya fara shiga cikin jirgin. Suka shiga babban hatsari.
24. Almajiran suka je suka tashe shi daga barci, suka ce, “Ubangiji, Ubangiji, za mu nutse!” Ya tashi ya kwaɓe iskar da kuma haukar ruwayen. Sai ruwayen da iskar suka natsu. Kome ya yi tsit.
25. Sai ya tambayi almajiransa, “Ina bangaskiyarku?” A cikin tsoro da mamaki, suka ce wa junansu, “Wane ne wannan? Yana ba da umarni ga iska da ruwa ma, kuma suna biyayya da shi?”