A A A A A

Luka 7:31-50
31. “To, da me zan kwatanta mutanen zamanin nan? Kamar me suke?
32. Suna kama da yaran da suke zama a bakin kasuwa, suna kiran juna, suna cewa: “ ‘Mun busa muku sarewa, amma ba ku yi rawa ba, Mun kuma yi muku waƙar makoki, ba ku kuma yi kuka ba.’
33. Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo, ba ya cin burodi, ba ya shan ruwan inabi, sai kuka ce, ‘Ai, yana da aljani.’
34. Ɗan Mutum ya zo yana ci, yana sha, sai kuka ce, ‘Ga mai yawan ci, mashayi, da kuma abokin masu karɓar haraji da “masu zunubi.” ’
35. Amma akan tabbatar da hikima ta gaskiya bisa ga dukan ʼyaʼyanta.”
36. To, ana nan, sai ɗaya daga cikin Farisiyawa ya gayyaci Yesu cin abincin yamma a gidansa, ya kuwa tafi gidan Bafarisiyen, ya zauna a tebur.
37. Da wata mace wadda ta yi rayuwar zunubi a wannan gari ta ji Yesu yana cin abinci a gidan Bafarisiyen, sai ta kawo ɗan tandun turaren alabasta,
38. ta kuma tsaya daga bayansa, wajen ƙafafunsa tana kuka, sai hawayenta sun fara zuba a ƙafafunsa. Sai ta goge su da gashin kanta, ta yi sumbace su, saʼan nan ta shafa musu turare.
39. Da Bafarisiyen da ya gayyace shi, ya ga wannan, sai ya ce a ransa, “Da mutumin nan annabi ne, da ya san ko wace ce take taɓansa, da kuma irin macen da take--cewa mai zunubi ce.”
40. Sai Yesu ya ce masa, “Siman, ina da abin da zan faɗa maka.” Shi kuwa ya ce, “Malam sai ka faɗa.”
41. Yesu ya ce, “An yi waɗansu mutum biyu da suke riƙe bashin mai ba da rance. Ana bin guda dinari ɗari biyar, ɗayan kuma hamsin.
42. Dukan biyun suka gagara biyansa, sai ya yafe musu. To, a ganinka, wa zai fi ƙaunar mutumin nan?”
43. Siman ya amsa, ya ce, “A ganina, wanda aka yafe wa mai yawa ne.” Sai Yesu ya ce, “Ka faɗi daidai.”
44. Sai ya juya wajen macen, ya ce wa Siman, “Ka ga macen nan? Na shigo gidanka, ba ka ba ni ruwa don ƙafafuna ba, amma ta wanke ƙafafuna da hawayenta, ta kuma goge su da gashin kanta.
45. Ba ka yi mini sumba ba, amma tun shigowata a nan, macen nan ba ta daina sumbar ƙafafuna ba.
46. Ba ka shafa mai a kaina ba, amma ta zubo turare a ƙafafuna.
47. “Saboda haka ina gaya maka, zunubanta masu yawa, an gafarta mata--gama ƙaunarta mai yawa ce. Amma wanda aka gafarta wa kaɗan kuwa, yakan nuna ƙauna kaɗan.”
48. Sai Yesu ya ce mata, “An gafarta miki zunubanki.”
49. Sauran baƙin suka fara ce wa juna, “Wane ne wannan, wanda har yake gafarta zunubai?”
50. Yesu ya ce wa macen, “Bangaskiyarki ta cece ki, ki tafi da salama.”