English
A A A A A

Luka 20:27-47
27. Waɗansu Sadukiyawa da suke cewa, ba tashin matattu, suka zo wurin Yesu da tambaya cewa,
28. “Malam, Musa ya rubuta mana cewa, ‘In ɗanʼuwan wani mutum ya mutu, ya bar mata amma ba ʼyaʼya, dole mutumin ya aure gwauruwar, ya samo wa ɗanʼuwansa ʼyaʼya.’
29. To, an yi waɗansu ʼyanʼuwa bakwai. Na fari ya auri wata mace, ya mutu ba ʼyaʼya.
30. Na biyun,
31. da na ukun suka aure ta. Haka nan dukansu bakwai suka mutu babu ʼyaʼya.
32. A ƙarshe, ita macen ma ta mutu.
33. Shin, a tashin matattu, matar wa za ta zama? Tun da su bakwan nan, sun aure ta.”
34. Yesu ya amsa, ya ce, “Mutanen zamanin nan suna aure, suna kuma ba da aure,
35. amma su waɗanda aka ga sun cancantar kasancewa a zamanin can, da kuma na tashin matattu, ba za su yi aure, ko su ba da aure ba.
36. Kuma ba za su sāke mutuwa ba, gama su kamar malaʼiku ne. Su ʼyaʼyan Allah ne, tun da su ʼyaʼyan tashin matattu ne.
37. Amma bisa ga labari na bishiya nan, mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, ko Musa ma, ya nuna cewa, matattu suna tashi. Gama ya kira Ubangiji, ‘Allah na Ibrahim, da Allah na Ishaku, da kuma Allah na Yaƙub.’
38. Shi ba Allah na matattu ba ne, amma na masu rai ne, gama a gare shi, duka na da rai.”
39. Sai waɗansu malaman dokoki suka amsa suka ce, “Ka faɗi daidai, malam!”
40. Kuma ba wanda ya sami ƙarfin halin yin masa waɗansu tambayoyi.
41. Sai Yesu ya ce musu, “Yaya suke cewa, ‘Kiristi ɗan Dawuda ne?’
42. Dawuda da kansa ya faɗa a cikin Zabura: “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina: “Zauna a hannun damana,
43. sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.” ’
44. Dawuda ya kira shi ‘Ubangiji.’ Ta, yaya zai zama ɗansa?”
45. Yayinda dukan mutane suna cikin sauraronsa, sai Yesu ya ce wa almajiransa,
46. “Ku yi hankali da malaman dokoki. Sukan so sa manyan riguna suna zaga, suna shaʼawan karɓan gaisuwa a wuraren kasuwanci, da kuma wuraren zama mafi daraja a majamiʼu, da wuraren ban girma a bukukuwa.
47. Suna mamaye gidajen gwauraye, kuma don burga, suna dogayen adduʼoʼi. Ga irin waɗannan mutane, za a yi musu hukunci mai tsanani sosai.”