English
A A A A A

Luka 7:1-30
1. Bayan Yesu ya gama gaya wa mutanen dukan waɗannan abubuwa, sai ya shiga Kafarnahum.
2. A can, akwai wani bawan wani jarumin yana ciwo, yana kuma a bakin mutuwa. Maigidansa kuwa yana sonsa sosai.
3. Jarumin sojan ya ji labarin Yesu, sai ya aiki waɗansu dattawan Yahudawa wajensa, yana roƙonsa yǎ zo yǎ warkar da bawansa.
4. Da suka isa wurin Yesu, sai suka roƙe shi sosai, suka ce, “Wannan mutum, ai, ya dace a yi masa haka,
5. domin yana ƙaunar alʼummarmu ta Yahudawa, har ya gina majamiʼarmu.”
6. Sai Yesu ya tafi tare da su. Da ya yi kusa da gidan, sai jarumin nan, ya aiki abokai su ce masa: “Ubangiji, kada ka dami kanka, gama ban isa ka shiga gidana ba.
7. Shi ya sa ban ma ga na isa in zo wurinka ba. Amma ka yi magana kawai, bawana zai warke.
8. Gama ni kaina, mutum ne a ƙarƙashin iko, akwai kuma sojoji a ƙarƙashin ikona. Nakan ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai yǎ tafi, ga wani kuma in ce, ‘Zo nan,’ sai yǎ zo. Nakan kuma ce wa bawana, ‘Yi abu kaza,’ sai yǎ yi.”
9. Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki sosai. Ya juya ya wa taron da yake binsa, “Ina faɗa muku, ban taɓa samun irin bangaskiya mai girma haka ko cikin Israʼila ba.”
10. Sai mutanen da aka aika, suka koma gida, suka tarar bawan ya warke.
11. Ba a daɗe ba, sai Yesu ya tafi wani garin da ake kira Nayin. Almajiransa da taro mai yawa suka tafi tare da shi.
12. Da ya yi kusa da ƙofar garin, sai ga wata gawa ana fitowa da ita. Shi ne ɗa kaɗai ga mahaifiyarsa, ita kuma gwauruwa ce. Taro mai yawa daga garin yana tare da ita.
13. Da Ubangiji ya gan ta, sai ya ji tausayinta, ya ce, “Kada ki yi kuka.”
14. Yesu ya je ya taɓa akwatin gawar, sai masu ɗaukarsa suka tsaya cik. Sai ya ce, “Saurayi, na ce maka, tashi!”
15. Sai mamacin ya tashi zaune, ya fara magana. Yesu kuma ya ba da shi ga mahaifiyarsa.
16. Sai tsoro ya kama su duka, suka yabi Allah, suna cewa, “Babban annabi ya bayyana a cikinmu. Allah ya zo domin yǎ taimaki mutanensa.”
17. Wannan labarin game da Yesu, ya bazu koʼina a Yahudiya da kewayenta.
18. Almajiran Yohanna suka gaya masa dukan waɗannan abubuwa. Sai ya kira biyu daga cikinsu,
19. ya aike su wurin Ubangiji, su tambaya su ce, “Kai ne wanda zai zo, ko kuma mu saurari wani dabam?”
20. Da mutanen suka iso wurin Yesu, sai suka ce, “Yohanna Mai Baftisma ne ya aike mu wurinka, mu yi tambaya, ‘Ko kai ne wanda zai zo, ko kuma mu saurari wani dabam?’ ”
21. A daidai lokacin nan, Yesu ya warkar da mutane da yawa masu ciwo, masu cututtuka, da kuma masu mugayen ruhohi. Ya kuma ba makafi da yawa ganin gari.
22. Sai ya amsa wa almajiran Yohanna, ya ce, “Ku koma ku faɗa wa Yohanna abin da kuka ji, da abin da kuka gani. Makafi suna ganin gari, guragu suna tafiya, ana warkar da waɗanda suke da kuturta, kurame suna ji, ana ta da matattu, ana kuma yi wa matalauta waʼazin bishara.
23. Mai albarka ne mutumin da bai yi shakkar bangaskiyar da yake da ita a kaina ba.”
24. Bayan almajiran Yohanna suka tafi, sai Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yohanna, ya ce: “Me kuka je ƙallo a hamada? Ciyawar da iska take kaɗawa ne?
25. In ba haka ba, to, me kuka je ƙallo? Mutum mai sanye da tufafi masu kyau ne? Aʼa, masu sa kayan tsada da suke cikin annashuwa, ai, a fada suke.
26. Amma me kuka je ƙallo? Annabi? I, ina kuma faɗa muku, ya ma fi annabi.
27. Wannan shi ne wanda aka rubuta game da shi, cewa: “ ‘Zan aiko da ɗan saƙona yǎ sha gabanka, wanda zai shirya hanya, a gabanka.’
28. Ina faɗa muku, a cikin duk waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya fi Yahaya girma. Duk da haka wanda ya fi ƙasƙanta a Mulkin Allah ya fi shi.”
29. (Dukan mutane, har da masu karɓar haraji, da suka ji kalmomin Yesu, sai suka yarda cewa hanyar Allah gaskiya ce, domin Yohanna ne ya yi musu baftisma.
30. Amma Farisiyawa da masanan dokoki, suka ƙi nufin Allah game da su, domin Yohanna bai yi musu baftisma ba.)