A A A A A

Luka 20:1-26
1. Wata rana da Yesu yana koyar da mutane, yana musu waʼazin bishara a filin haikalin, sai manyan firistoci da malaman dokoki, tare da dattawan suka zo wurinsa.
2. Suka ce masa, “Gaya mana, da wane iko kake yin waɗannan abubuwa. Wa ya ba ka wannan ikon?”
3. Ya amma ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. Ku faɗa mini,
4. baftismar Yohanna, daga sama ne ta fito, ko kuwa daga wurin mutane ne?”
5. Sai suka yi shawara da junansu, suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama ne,’ zai tambaya, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’
6. Amma in kuma muka ce, ‘Daga mutane ne,’ dukan mutanen za su jajjefe mu da duwatsu, domin sun tabbata cewa, Yohanna annabi ne.”
7. Don haka, sai suka amsa cewa, “Ba mu san inda ta fito ba.”
8. Yesu ya ce, “To, ni ma ba zan gaya muku, ko da wane iko ne, nake yin waɗannan abubuwa ba.”
9. Sai ya ci gaba da gaya wa mutanen wannan misali, ya ce, “Wani mutum ya yi gonar inabi, sai ya ba da hayarta ga waɗansu manoma, saʼan nan ya yi wata doguwar tafiya.
10. A lokacin girbi, sai ya aiki bawa zuwa wurin masu hayan, don su ba shi daga cikin ʼyaʼyan inabin. Amma ʼyan hayan suka yi wa bawan nan duka, suka kore shi hannu wofi.
11. Ya sāke aikan wani bawa, shi ma suka yi masa duka, suka kunyata shi, suka kuma kore shi hannu wofi.
12. Har yanzu, ya sāke aikan na uku, amma suka ji masa rauni, suka jefar da shi waje.
13. “Sai mai gonar inabin ya ce, ‘Me zan yi? Zan aiki ɗana da nake ƙauna, wataƙila za su girmama shi.’
14. “Amma da ʼyan hayan suka gan shi, sai suka tattauna zancen, suka ce, ‘Wannan shi ne magājin, mu kashe shi saʼan nan gādon zai zama namu!’
15. Sai suka fitar da shi waje, suka kashe shi. “To, me mai gonar inabin zai yi da su?
16. Zai zo ya karkashe masu hayan nan, ya ba wa waɗansu gonar inabin.” Da mutanen suka ji wannan, sai suka ce, “Allah ya sawwaƙa!”
17. Yesu ya zura musu ido, ya ce, “To, mene ne maʼanar abin da aka rubuta cewa, “ ‘Dutsen da magina suka ƙi, shi ne kuwa ya zama dutsen kan ginin  ’?
18. Duk wanda ya fāɗi a kan dutsen nan, zai kakkarye. Kuma in dutsen nan ya fāɗi a kan wani, zai murƙushe shi.”
19. Malaman dokoki da manyan firistoci, suka nemi hanyar kama shi nan da nan, domin sun san cewa, ya yi wannan misali a kansu ne, amma suna jin tsoron mutane.
20. Sai suka sa masa ido, suka aiki ʼyan leƙen asiri, waɗanda suka nuna kamar su masu gaskiya ne, suna nufin su kama shi game da abin da zai faɗa, domin su ba da shi ga gwamna mai mulki, da mai iko.
21. Sai ʼyan leƙen asirin suka tambaye shi, suka ce, “Malam, mun sani kana faɗin, kuma kana koyar da abin da yake daidai, ba ka kuma nuna bambanci, amma kana koyar da hanyar Allah bisa ga gaskiya.
22. Daidai ne mu biya haraji ga Kaisar, ko babu?”
23. Ya gane makircinsu, sai ya ce musu,
24. “Nuna mini dinari. Hoton wane ne, kuma rubutun wane ne a kai?”
25. Suka amsa, “Na Kaisar.” Sai ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.”
26. Ba su iya kama shi a kan abin da ya faɗa a fili ba. Amsarsa ya ba su mamaki, shi ya sa suka yi shiru.