A A A A A

Luka 19:28-48
28. Bayan Yesu ya yi wannan magana, sai ya yi gaba zuwa Urushalima.
29. Da ya kai kusa da Betfaji da Betani, a tudun da ake kira Dutsen Zaitun, sai ya aiki almajiransa guda biyu, ya ce musu,
30. “Ku je ƙauyen da yake gaba da ku. Da kuna shiga, za ku tarar da wani ɗan jaki, wadda ba wanda ya taɓa hawa, a ɗaure a wurin. Ku kunce shi ku kawo nan.
31. In wani ya tambaye ku, ‘Don me kuke kunce shi?’ Ku ce masa, ‘Ubangiji yana bukatarsa.’ ”
32. Waɗanda aka aika su yi gaba suka tafi, suka kuwa tarar kamar yadda ya gaya musu.
33. Suna cikin kunce ɗan jakin, sai masu ɗan jakin suka ce musu, “Don me kuke kunce shi?”
34. Suka amsa suka ce, “Ubangiji ne na bukatarsa.”
35. Suka kawo shi wurin Yesu. Suka sa rigunarsu a kan ɗan jakin, saʼan nan suka sa Yesu a kai.
36. Yana cikin tafiya, sai mutane suka shimfiɗa rigunarsu a kan hanya.
37. Da ya yi kusa da wurin da hanyar ta gangara zuwa Dutsen Zaitun, sai dukan taron almajirai suka fara yabon Allah, da muryoyi masu ƙarfi, da murna, saboda dukan ayyukan banmamaki da suka gani.
38. Suna cewa, “Mai albarka ne sarki wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji! Salama ta kasance a sama, da ɗaukaka kuma a can cikin sama!”
39. Sai waɗansu Farisiyawa a cikin taron suka ce wa Yesu, “Malam, ka kwaɓi almajiranka!”
40. Ya amma ya ce, “Ina gaya muku, ko da sun yi shiru, duwatsu za su fara kirari.”
41. Da ya yi kusa da Urushalima, ya kuma ga birnin, sai ya yi kuka a kanta,
42. kuma ya ce, “In ke, ko ke ɗin ma, dā ma kin san abin da zai kawo miki salama a wannan rana, amma yanzu an ɓoye shi daga idanunki.
43. Ranakun za su auko miki, a lokacin da abokan gābanki za su gina bango gāba da ke, su kuma kewaye inda kike, za su kuma tsare kowane gefenki, su sa ke a tsakiya.
44. Za su fyaɗa ke a ƙasa, ke da ʼyaʼyan da suke cikin katanganki. Ba za su bar wani dutse a kan wani ba, saboda ba ki gane da lokacin da Allah zai ziyarce ki ba.”
45. Sai ya shiga filin haikali, ya fara korar masu sayar da kaya.
46. Ya ce musu, “A rubuce, yake cewa, ‘Gidana, zai zama gidan adduʼa,’ amma ga shi kun mai da shi ‘kogon ʼyan fashi.’ ”
47. Kowace rana, ya yi ta koyarwa a haikalin. Amma manyan firistoci, da malaman dokoki, da shugabannin mutane, suna ƙoƙarin kashe shi.
48. Amma ba su sami hanyar yin haka ba, domin kalmominsa sun kama hankalin dukan mutanen.