A A A A A

Luka 19:1-27
1. Yesu ya shiga Yeriko, yana ratsa ta cikinta.
2. Akwai wani mutum a garin, mai suna Zakka. Shi shugaban masu karɓar haraji ne, mai arziki kuma.
3. Ya so ya ga ko wane ne Yesu, amma saboda taron, bai iya ba, domin shi gajere ne.
4. Saboda haka, ya yi gaba da gudu, kuma ya hau itacen sikamo, don ya gan shi, tun da Yesu zai bi wannan hanyar ne.
5. Da Yesu ya iso wurin, sai ya ɗaga ido sama, ya ce masa, “Zakka, ka yi maza ka sauka. Ni kam, dole in sauka a gidanka yau.”
6. Sai ya sauka nan da nan, ya karɓe shi da murna.
7. Dukan mutane suka ga haka, kuma suka fara gunaguni, suka ce, “Ya je don ya zama baƙon ‘mai zunubi.’ ”
8. Amma Zakka ya tashi a tsaye, ya ce wa Ubangiji, “Duba, Ubangiji! Nan take, rabin dukiyar da nake da shi, na ba wa matalauta. In kuma na taɓa cutan wani, a kan wani abu, zan mayar da shi ninki huɗu.”
9. Sai Yesu ya ce masa, “Yau, ceto ya zo gidan nan, domin wannan mutum shi ma ɗan Ibrahim ne.
10. Saboda Ɗan Mutum ya zo ne, domin ya nemi abin da ya ɓata, ya cece shi kuma.”
11. Yayinda suna cikin sauraron wannan, sai ya ci gaba da gaya musu wani misali, domin ya yi kusa da Urushalima, kuma mutanen suna tsammani mulkin Allah zai bayyana, nan da nan.
12. Ya ce: “Wani mutum mai martaba ya tafi wata ƙasa mai nisa don a naɗa shi sarki saʼan nan ya dawo.
13. Saboda haka ya kira bayinsa goma ya ba su mina goma. Ya ce, ‘Ku yi kasuwanci da kuɗin nan, sai na dawo.’
14. “Amma talakawansa suka ƙi shi, sai suka aikar da wakilai bayansa, domin su ce, ‘Ba mu son wannan mutum ya zama sarkinmu.’
15. “Duk da haka, aka naɗa shi sarki, saʼan nan ya dawo gida. Sai ya aika aka kira bayin da ya ba su kuɗin, don ya san ribar da suka samu.
16. “Na fari ya zo, ya ce, ‘Ranka yǎ daɗe, minarka ya sami ribar goma.’
17. “Maigidan ya amsa, ya ce, ‘Madalla, bawana mai kirki! Tun da ka yi aminci a kan abu ƙanƙani, ka yi riƙon birane goma.’
18. “Na biyun ya zo, ya ce, ‘Ranka yǎ daɗe, minarka ya sami ribar biyar.’
19. Maigidansa ya ce, ‘Kai ka yi riƙon birane biyar.’
20. “Sai wani bawan ya zo, ya ce, ‘Ranka yǎ daɗe, ga minarka. Na ɓoye shi a wani ɗan tsumma.
21. Na ji tsoronka, don kai mai wuyan shaʼani ne. Kakan ɗauki abin da ba ka ajiye ba, kakan kuma yi girbin abin da ba ka shuka ba.’
22. “Sai maigidansa, ya amsa, ya ce, ‘Zan hukunta ka a kan kalmominka, kai mugun bawa! Ashe, ka san cewa ni mai wuyan shaʼani ne, nakan ɗauka abin da ban ajiye ba, ina kuma girbin abin da ban shuka ba?
23. Don me ba ka sa kuɗina a wajen ajiya, don in na dawo, in sami riba a kai ba?
24. “Sai ya ce wa waɗanda suke tsaye a wajen, ‘Ku karɓi minarsa ku ba wa wanda yake da mina goma.
25. “Suka ce, ‘Ranka yǎ daɗe, ai, yana da guda goma ko!’
26. “Ya amsa ya ce, ‘Ina gaya muku, duk wanda yake da abu, za a ƙara masa. Amma wanda ba shi da shi kuwa, ko abin da yake da shi ma, za a karɓe.
27. Amma waɗannan abokan gābana, waɗanda ba su so in zama sarkinsu ba, ku kawo su nan, ku karkashe su, a gabana.’ ”