A A A A A

Luka 18:24-43
24. Yesu ya kalle shi, ya ce, “Yana da wuya fa, masu arziki su shiga mulkin Allah!
25. Hakika, zai fi sauƙi raƙumi ya shiga ta ƙofar idon allura, da mai arziki ya shiga mulkin Allah.”
26. Mutanen da suka ji wannan magana suka tambaya suka ce, “To, in haka ne, wa zai iya samun ceto?”
27. Yesu ya amsa, ya ce, “Abin da ba ya yiwuwa ga mutane, mai yiwuwa ne ga Allah.”
28. Sai Bitrus ya ce, masa, “To, ga shi mun bar kome da muke da shi, don mu bi ka!”
29. Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, ba wanda ya bar gida, ko mata, ko ʼyanʼuwa maza, ko iyaye, ko yara, saboda mulkin Allah,
30. da zai kāsa samun riɓi mai yawa, a wannan zamani, ya kuma sami rai madawwami a zamani mai zuwa.”
31. Sai ya kai Sha Biyun gefe ɗaya, ya ce musu, “Za mu Urushalima, kuma dukan abin da annabawa suka rubuta a kan Ɗan Mutum zai cika.
32. Za a ba da shi ga Alʼummai, za su yi masa baʼa, su zage shi, su tofa masa miyau, su yi masa bulala, su kuma kashe shi,
33. a rana ta uku kuma zai tashi.”
34. Almajiran ba su gane da ko ɗaya daga cikin wannan ba. An ɓoye musu maʼanarsa, kuma ba su gane da abin da yake magana a kai ba.
35. Da Yesu ya yi kusa da Yeriko, akwai wani makaho da yake zaune a gefen hanya, yana bara.
36. Da ya ji taron suna wucewa, sai ya yi tambaya ko mene ne ke faruwa.
37. Suka ce masa, “Ai, Yesu Banazare ne ke wucewa.”
38. Sai ya yi kira, ya ce, “Yesu, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!”
39. Mutane da suke gaba suka kwaɓe shi, suka ce masa ya yi shiru. Amma sai ya ƙara ɗaga murya, yana cewa, “Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!”
40. Sai Yesu ya tsaya, ya ba da umarni a kawo mutumin wurinsa. Da ya zo kusa, Yesu ya tambaye shi, ya ce,
41. “Me kake so in yi maka?” Sai ya amsa, ya ce, “Ubangiji, ina so in sami ganin gari.”
42. Yesu ya ce masa, “Ka sami ganin garinka. Bangaskiyarka ta warkar da kai.”
43. Nan da nan, ya sami ganin garinsa, kuma ya bi Yesu, yana yabon Allah. Da dukan mutane suka ga wannan, sai su ma suka yabi Allah.